✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don Uwargida: Hikimomin Zama da miji (1)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan hikimomin da uwargida za ta yi amfani da su don samun sauki da aminci cikin rayuwar aurenta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

 

Hikima ta 2: Yi domin Allah:

Kamar yadda bayani ya gabata kan yadda uwargida za ta zabo dabi’u mafi muhimmanci ga maigidanta ta rika dabbakar da su cikin zamantakewar aurenta, man fetur din da zai kara wa hikimar farko aminci, karko da karfin tasiruntuwa shi ne ‘yi domin Allah.’ Lallai yi domin Allah da bari domin Allah sirrin kyautata rayuwa gaba dayanta ne ba ma rayuwar aure kadai ba. Don fahimtar wannan hikima da samun saukin dabbaka da ita cikin zamantakewar aure, uwargida sai ta yi nazari da kokarin aiwatar da wadannan abubuwa a kodayaushe:

1. Aure ibadah ne: Mancewa da muhimmancin aure a matsayinsa na ibada kamar sauran ibadoji, na daya daga cikin manyan matsalolin auratayya a wannan zamani. Saboda ma’aurata ba su daukar auratayyarsu da muhimmanci na ‘Bautar Ubangiji’ kamar yadda suka ba Sallah, azumi zakka da Hajji wannan muhimmanci, shi ke sa da yawan ma’aurata suke wa auratayyarsu rikon sakainar kashi. Hanyar more wa rayuwar aure shi ne yin ta domin Allah, don haka ko murmushi za ki yi ga fuskar mijinki, ki kudurta a ranki da niyyar ibada, to za ki ci riba biyu ke nan.

2. Kamar yadda komai tsanani rayuwa, canzawar yanayi da cabewar al’amura , dole Musulmi ya gabatar da Sallah da sauran ibadu, to haka kuma komai tsananin da ya riski uwargida cikin rayuwar aurenta bai kamata hakan ya sa ta daina gabatar da kyakykyawar dabi’a ga maigidanta ba; wannan shi ne babban sirrin ‘yi domin Allah,’ kina aiwatar da  komai na rayuwar aurenki domin Allah to ladanki na ga Allah, in hakan ya samar maki da kyakykyawar kulawa daga maigida, wannan karin dadi ne, in kuma kika sami akasin haka, kada haka ya sa ki canza domin ‘don Allah kike yi’ ba don burge Maigida kadai ba.

3. Rashin yi domin Allah asara ce babba kuma hanyar tara bakin ciki mai yawa cikin rayuwar aure ce, domin  dan adam da halayyarsa ba su da tabbas, suna iya canzawa a kowane lokaci; in kika huldaci Maigida da kyakykyawar dabi’a don kawai biyan bukatarki, don ki kai ga wani matsayi, ko don ki samu wani abu wurin maigida, don ki mallake shi, don ke ma ya rika jiji da ke, don kar ya kara aure, da sauran dalilai makamanta, to mafi akasarin lokutta za ki kasance cikin bacin rai da takaici kodayaushe kika samu akasi a kan abin da kike fatar samu daga maigida. Amma in kin kudurta a ranki domin Allah za ki rika zartar da komai na cikin rayuwar aurenki, to takaicinki dan kadan ne domin koda maigida bai saka maki da kyautatawa ba, Allah zai ba ki lada kuma zai saka maki da mafi kyawun sakamako.

Hikima ta 3: Hanya, kuma kofar Aljannarki: Misali a ce miki ga wata hanya mai cike da matsaloli, ga duhu, ga kayoyi ga abubuwan fargaba, amma in kika daure ki bi ta ba tare da karkata ba za ta kai ki har cikin fankamemen gida mai fadin sama da kasa gaba dayansu; in kuma kika ki bin ta, ko kika karkace daga gareta, to wutar jahannama za ki fada inda za a azabtar dake har fatar jikinki ta narke a sake halitta maki, shin wace hanya za ki bi? Ai tabbas ba wacce za ta yarda ta yi kuskuren kin bin wannan hanya ko ta karkace mata. Kuma a ce ga gidanki nan a Aljanna, amma kofar bude ta shi ne hakuri da kyautata dabi’a ga mijinki, in kuma kika rasa wannan mabudi to kamar kin tanadar wa kanki matsugunni ne a wuta. Tabbas ba darajar da ta kai dacewa da gidan Aljanna ni’ima da kuma kubuta daga wuta, wannan shi ne girman darajar mijinki a gareki yake uwargida, don haka ba abin wasa ba ne, ba abin yi wa ragwanci ba ne, abu ne da za ki ba shi muhimmanci sama da kowace harka ta rayuwarki bayan bautar Allah Madaukakin Sarki.

Uwargida ta rike wannan a zuciyarta, ta rika tunano alfanun wannan a kodayaushe, musamman lokacin da abubuwa suka yi zafi, nauyi ko suka rincabe cikin rayuwar aurenta, sai uwargida ta tunano cewa hakuri, dauriya da sadaukarwarta in ta kamantasu da sakamakon da za ta samu na gidan Aljannar ni’ima karshen dukkan wani kunci wahala ko rashin jin dadi.

Sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.