Alhaji Abubakar Aminu shi ne Shugaban kungiyar Information Nigeria (I-Nigeria) na Arewacin Najeriya. A lokacin da ya tattauna da ’yan jarida a Abuja a ranar Juma’a ya ce, sun kafa kungiyarsu ne don wayar da kan jama’a kan illar da ke cikin watsa labaran da ke muzanta Najeriya. Ya ce, kungiyarsu na ba da muhimmiyar gudunmawa wajen ganin an samu ingantaccen tsaro a kasar nan.
Mene ne dalilin kafa kungiyar I-Nigeria?
kungiyar I-Nigeria, kungiya ce ta fitattun ’yan Najeriya masu kishin kasa karkashin jagorancin shugabarta ta kasa Ada Stella Apiafi, mun zauna don mu ga yadda za mu samar da hadin kai a kasar nan da kuma yadda za mu canja tunani da munanan akidun da ake kallon kasar mu da shi. Sau da yawa idan ka fita kasashen waje za ka tarar labaran da suke fitowa daga Najeriya ba masu dadi ba ne, da hannunmu muke rubuta munanan labari a kan kasar nan, ba ma tunanin wane irin suna muke ba kanmu. Mu da muke tafiye-tafiye hakan na damunmu, sai muka ga to shin za a ci gaba da zama a haka? Me yiwuwa da yawa daga cikinmu ba sa fita, suna rayuwarsu kawai a Najeriya ne, kuma ba sa ganin illar da suke janyo wa kasar nan, hakan ya sa muka kafa wannan kungiyar don mu rika jan hankalinsu kan irin wadannan munanan akidu da kuma kalamai.
Tun yaushe kuka kafa kungiyar I-Nigeria, kuma wane ayyuka take gabatarwa?
Zuwa yanzu mun kai shekara biyu zuwa uku, sannan a bangaren ayyuka mun samu nasarori masu yawa, kadan daga ciki su ne, mun zazzaga gidajen jaridu, musamman wadanda muka fahimci ’yan Najeriya na bibiyar labaransu, mun yi musu bayani game da I-Nigeria, sun buga labaran, kuma jama’a da dama sun karanta, sun kuma fa’idantu. Sannan muna sa talla a gidajen rediyo, inda cikin tallar muke nuna wa mutanen Najeriya cewa akwai bukatar mu hada kai tare da kishin kasarmu, ya kamata mu rika tunanin abubuwa masu kyau kan kasarmu; mu daina zagin kasar mu, ko muna ganin shugabanninmu su ne suka fi sauran shugabanni lalacewa a duniya. Su ma sauran kasashen suna da irin wadannan shugabanni, abin da suke yi kawai shi ne, suna yin shiru ne, kuma sun fi mu sanin hanyoyin da za su yi magana da shugabanninsu. Amma mu sai ka ji ana cewa ai shugaba wane da shi da Fir’auna tafiyarsu daya. Ko shugaba wane su ne irin wadanda aka tsinewa. Ko shugaba wane ba addinin Musulunci yake yi ba, a matsayinmu na mabiya addinai mun san abubuwa da addinanmu suka ce mana. Addinanmu sun yi mana wa’azi kan cewa kamata ya yi mu zama masu yi wa shugabannin mu addu’o’i ba mu zama masu tsine musu ba.
Sannan a yanzu mun kai wa makarantu a birnin tarayya Abuja ziyara, mun rubuta wa Ministan Abuja Dokta Bala Muhammad takarda, inda muka sanar da shi ayyukanmu, kuma ya ba mu goyon baya da hadin kai, sannan ya hada mu da hukumar ilimi ta birnin tarayya. Yara da matasa muke ganin ya kamata a fara canja musu irin wannan tunani. A yanzu dai mun samu makarantu kamar guda uku a Abuja, inda muka kafa kungiya I-Nigeria Club, sannan kusan kowane karshen wata muna zama mu tattauna tare da su, mu bayyana musu abubuwan da suke faruwa a Najeriya, sannan muna nuna musu tunanin da ya kamata su sa a gabansu a matsayin su na yara manyan gobe. Sannan akwai shirin da muke gabatarwa a gidan talabijin kowace Alhamis a Channel 24, karfe 8:30 na dare zuwa 9:00, shi ma shiri ne da muke yi kan wayarwa tare da ilimintar da ’yan Najeriya kan bukatun canja halayenmu da yadda ya kamata kowane dan kasa ya kasance da irin gudunmawar da ya kamata ya bayar.
Haka kuma kungiyar I-Nigeria tana daukar nauyin masu magana da yawun hukumomin jami’an tsaro na kasa, dukkan ranakun Laraba, mukan kawo jami’i ya zo nan a tara ’yan jarida don ya yi musu bayani, su kuma ’yan jaridar su yi masa tambayoyi. A yanzu idan kuka lura Najeriya tana fama da matsalar rashin tsaro, kuma akwai bukatar mu ga cewa mutane sun san irin kokarin da gwamnati da jami’an tsaron suke yi don dakile matsalar tsaro.
A yanzu wadanne irin matsaloli kuke fuskanta?
Matsalarmu ita ce, ’yan jarida ba sa daukar sakonnin ilimintarwar da muke yi su aika zuwa ga jama’ar da aka yi domin su, daya daga cikin matsalolin da muke fama da su ke nan.
Ga shi I-Nigeria ta kai kusan shekara uku da kafuwa kuna da membobi akalla nawa?
Babu shakka idan ka dubi membobinmu a shafin sada zumunta na Facebook a yanzu za ka samu mutane sama da dubu biyar, sannan akwai wadanda suka rubuto mana suna son ba da gudunmawarsu kan ayyukan kungiyar.
Ina kungiyar take samun kudin da take gudanar da ayyukanta?
Saboda kishin kasa, daga aljihunmu muke cire duk wani kudi da za a yi wani ai ki