Alhaji Armaya’u Yahaya shi ne shugaban kungiyar ’yan kasuwar Wunti da ke Jihar Bauchi, har ila yau, shi ne mataimakin shugaban ‘yan kasuwa reshen Arewa-maso-Gabas cikin tattaunawarsu da wakilinmu ya yi tsokaci game da halin da ‘yan kasuwar arewa suke ciki da sauran batutuwa: Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Alhaji Arma Ya’u: Sunana Alhaji Armaya’u Yahaya mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu reshen Arewa-maso-Gabas wannan kungiya tana daya daga cikin kungiyoyin da suke ba da gagarumar gudunmawa wajen magance matsalar zaman kashe wando a tsakanin matasan arewa. Kuma a matsayina na tsohon dan kasuwa na jima ana fafatawa da ni a siyasa, amma daga bangaren adawa wato tun lokacin ANPP zuwa CPC har zuwa kafa jam’iyyar APC.
Da yawa daga cikin ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati da kowa da kowa duk wanda ya samu kudi mai kauri bashi da wajen zuwa sai kasuwa domin anan ne ake kashe kudi da aka samu. Da ma’aikaci da ‘yan kasuwa kamar danjuma ne da dan jummai domin kowa na da matukar mahimmanci a tsarin zamantakewar rayuwa dan uwansa.
Aminiya: Me ne ne manufar kafa wannan kungiya?
Alhaji Arma Ya’u: Mun kafa wannan kungiya ne domin jawo ‘yan kasuwar Arewa-maso-Gabas da ke cikin harkokin siyasa a wannan shiyya da ke koma baya wajen kasuwanci kuma dole ‘yan kasuwa su tsunduma cikin siyasa.
Aminiya: Mambobin kungiyarku sun kai mutum nawa?
Alhaji Arma Ya’u: Maganar gaskiya muna da dimbin mambobi a kungiyar wanda ba za su lissafu ba. Dole sai an yi binciken sunayensu a rijistar wannan kungiya kafin a iya fahimtar hakan.
Aminiya: Me ye bukatarku ga gwamnonin shiyyar Arewa?
Alhaji Arma Ya’u: Abin da nake so gwamnonin Arewa su fara yi ga ‘yan kasuwa shi ne su taimaki wadanda suka musu wahala a lokacin kamfen domin yin haka shi ne zai nuna cewa tabbas an samu sabuwar gwamnati a Najeriya wadda take da kokarin kamanta adalci ga kowa da kowa.
Aminiya: Ta wasu hanyoyi kake ganin ‘yan kasuwa za su mori wannan gwamnati sabuwa?
Alhaji Arma Ya’u: Hanyoyin da ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu za su mori wannan gwamnati suna da matukar yawa domin na farko shi ne a sayi kayanmu ita ce hanya daya da fara amfana da gwamnati.Ta biyu idan aka sayi kayan da yawa daga cikinsu za su sake zuwa sari kasuwa kaga an amfana.
Aminiya: Me ne ne sakonka ga kananan ‘yan kasuwa masu tasowa?
Alhaji Arma Ya’u: Babban sakona ga kananan ‘yan kasuwa masu tasowa shi ne a rika tausayawa masu sayen kaya bayan haka muna kokonsu su ba da dukkan goyon bayansu ga sabuwa gwamnati domin tana da shirye-shirye masu kyau.
Aminiya: Akwai wasu kalubalen da kungiyarku take fuskanta a halin yanzu?
Alhaji Arma Ya’u: Babbar matsalar da wannan kungiyar take fuskanta a halin yanzu shi ne akwai dimbin ‘yan kasuwa wanda ba su da wani jari mai karfi a hannunsu sakamakon haka harkokinsu sun tsaya cak. Amma sabon gwamnan Jihar Bauchi da aka zaba ya yi alkawuran tallafa wa kananan ‘yan kasuwa sabanin yadda wadanda suka gabace shi suka gina wasu ‘yan tsiraru marassa kishin Jihar Bauchi. Ka ga misali Barista Abubakar lauya ne, amma idan yana magana akan kasuwanci sai kaji yana sosawa ‘yan kasuwa inda yake musu kaikayi. Allah Ya ba shi ikon cika alkawuran da ya dauka.
Aminiya: Akwai wata gudunmawa da kungiyarku ta bayar lokacin zaben shugaban kasar da ya gabata?
Alhaji Arma Ya’u: Hakika kungiyarmu mun ba da gudunmawa sosai a lokacin zaben shugaban kasa domin mun fadawa ‘yan a fili su zabi Janar Muhammadu Buhari domin shi ne bakaniken da zai iya gyara matsalolin ’yan Najeriya. Tun bayan kammala zaben, Masallatanmu da kasuwanni sun zauna lafiya. Hakazalika, tashoshin mota babu wata barazana a bangaren tsaro muna godiya ga Allah.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga wadanda aka zaba?
Alhaji Arma Ya’u: Babban sakona ga ‘yan siyasa kowa ya ga abin da ya faru a lokacin zabe saboda haka ya kamata su dauki darasi domin duk dan siyasar da ya yi kan kara ga talakawa, sai sun masa na ita ce.
Aminiya: Wane hali ‘yan kasuwar Jihar Bauchi suke ciki?
Alhaji Arma Ya’u: ‘Yan kasuwar Jihar Bauchi babu abin da suka amfana daga gwamnatin mai barin gado domin gwamna ya ba da bashin kudi, amma an raba wa wasu ‘yan tsiraru masu uwa a gindin murhu saboda haka ya dace yanzu a taimaki duka ‘yan kasuwa.
Aminiya: A karshe wane sako kake da shi ga ‘yan kasuwar Najeriya?
Alhaji Arma Ya’u: Ina kira da babbar murya ga ‘yan kasuwar Najeriya da mu ci gaba da yin addu’o’i na musamman ga sabon shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi. Kuma mu ’yan kasuwa za su ci gaba fatan Allah Ya kawo zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.