Tashe-tashen hankula sun mamaye Jihar Anambra, ta yadda tsaron rayuka da dukiyoyi ke fuskantar barazana yanzu.
Wadanda ake zargin mambobin haramtacciyar Kungiyar mai son Kafa kasar Biyafara (IPOB) ne suke tayar da hankula da aikata abubuwan ta’addanci a fadin jihar.
- Farashin danyen mai ya doshi $84 a kasuwar duniya
- Italiya na bincike kan nuna wariya ga Kalidou Koulibaly
Wannan ya yi mummunan tasiri a kan tattalin arziki da zamantakewa da al’adu, kamar yadda ya taba harkokin siyasa ciki har da gangami da kuma tarurruka.
Yanzu haka, motoci ko motocin alfarma irin su Jeep da manyan motoci ko duk wata mota da ke dauke da alamar wata jam’iyyar siyasa ko alamar gwamnati ko lambar masu kudi su ake kai wa hari.
Wannan lamari na ci gaba da haifar da fargaba a tsakanin mutane, lamarin ya sa jama’a da dama sun kasa ci gaba da gudanar da kasuwancinsu, inda hakan na iya yin mummunan tasiri ga zaben Gwamnan Jihar da ke tafe a ranar 6 ga Nuwamba.
A ranar Lahadin makon jiya, kungiyar ta’addancin ta kai hari tare da kona ’yan sanda da hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da gidan wani dan Jam’iyyar APC kuma mai ba da shawara ga Gwamnan Jihar Legas kan Magudanun Ruwa da Tsabtar Muhalli, Mista Joe Igbokwe a garin Nnewi.
Haka a ranar Alhamis din makon shekaran jiya, sun kai hari kan ayarin dan Majalisar Wakilta na mazabar Nnewi ta Arewa da Nnewi ta Kudu da Ekwusigo, Mista Chris Azubogu a yankin Nnobi na jihar, inda suka kashe direbansa.
A wannan Alhamis dai, a garinAjalli, hedkwatar Karamar Hukumar Orumba ta Kudu, sun kona ofishin ’yan sanda da ababen hawa a harabarsa, inda suka kashe ’yan sanda biyar tare da toshe babbar hanyar tarayya da ke cikin garin na tsawon awanni.
A daren Talatar da ta gabata, an kashe Dokta Chike Akunyili, mijin marigayiya tsohuwar Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) kuma Ministar Labarai, Farfesa Dora Akunyili, tare da direbansa da ’yan sanda masu kula da lafiyarsa.
Haka dai a ranar Talatar, an kashe wani sojan ruwa da ke aiki tare da Rundunar Sojojin Ruwa da ke Anacha, a yankin Iweka wadda cibiyar kasuwan ce yayin da kuma aka fille kan wani mutum a Obosi.
Haka kuma an kashe ’yan sanda uku.
Gwamna Willie Obiano na Jihar Anambra ya fada a ranar Laraba cewa a tsakanin Lahadi, 26 zuwa Laraba 29 ga Satumba, sama da mutum 10 aka kashe a yankuna daban-daban na jihar.
Halin da ake ciki a Jihar Anambra abin takaici ne yadda ake ta asarar rayuka, inda da kyar a ce rana ta bullo ta fadi ba tare da rahoton an kashe wani ba, wanda kuma za a iya kauce wa faruwar hakan.
Yaya za a bayyana kisan sama da mutum 10 cikin kwana uku? Dole ne a daina wannan kashe-kashe.
Tilas a yi kokarin kama masu aikata hakan. Kamar yadda aka sani gaba daya yankin Kudu maso Gabas yana cikin zaman lafiya har zuwa lokacin da ESN wadda reshe ne ta masu fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) ta fara kai hare-hare.
Wannan kungiyar ta shafe watanni da dama tana kai hare-hare a kan fararen hula da jami’an tsaro, tare da lalata kadarori.
Duk da cewa Kungiyar IPOB ta musanta zargin da kuma hannunta a cikin kisan da ke faruwa da alama jam’ian tsaro sun rasa iko, inda sojoji suke watsi da bindigoginsu suna tserewa maimakon kare fararen hula da dukiyoyinsu wanda hakki ne da ya rataya a wuyansu.
Haka zalika a ranar 24 ga Mayu, 2021, IPOB ta dauki alhakin kai hari kan ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Awka, babban birnin jihar, inda ta yada faya-fayen bidiyon hare-haren.
Haka kuma haramtacciyar kungiyar na shelanta cewa “Ba za a sake yin zabe a Jihar Anambra ba.”
Dole ne a dakatar da wannan cin mutunci da ake yi wa mutanen Jihar Anambra da yankin Kudu maso Gabas da kuma Najeriya cikin gaggawa.
Gwamnati ba za ta samu kwanciyar hankali ba a yayin da ake asarar rayuka.
Ya kamata a kira wannan aikin da sunan, ta’addanci kuma a dauki duk wani mataki da ya dace.
Duk wadanda suke da hannu cikin wadannan munanan ayyuka ya kamata a fallasa su, a kuma hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
Ya kamata Gwamnan Jihar Anambra ya yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro don kawo karshen wannan rikici.
Haka, ya kamata gwamnoni a yankin su taru su yi kokari don ganin sun dakatar da ayyukan wannan haramtatciyar kungiya take yi.