✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dole dan Kudu ya yi takarar shugaban kasa a APC —Gwamnonin Arewa ga Buhari

Ana zargin uwar jam'iyyar na neman ayyana Sanata Ahmad Lawana matsayin dan takara

Gwamnonin Jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya sun jaddada matsayarsu kan dan takarar shugaban kasa jam’iyar ya fito daga Kudu.

Gwamnoin kuma yi watsi da zabin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

Wannan sabon sa-toka-sa-katsi ya kunno kai ne a jajibirin gudanar da taron zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar mai mulki, bayan gwamnonin sun shaida wa Buhari cewa yankin Kudu ya kamata a bai wa takara.

A ganawarsu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, gwamnonin sun shaida mishi cewa ya zama wajibi a bar wa yankin Kudu damar fitar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne bayan bullar ji-ta-ji-tar cewa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar da sunan Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Amma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Gwamna Simon Lalong a Jihar Filato, ya ce a ganawar da suka yi da Buhari ranar Litinin, shugaban kasar ya nuna musu goyon bayan kan matakin da suka dauka.

Lalong, ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa cewa Buhari ya jaddada musu cewa wajibi ne a komai a fili wajen fitar da dan takarar shugaban kasa.

Ya bayyana cewa kuma a halin yanzu Buhari ba shi da dan takarar shugaban kasa, don haka ya bukaci gwamnonin su je su tattauna da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC) domin ganin tabbatuwar hakan.

Lalong ya ce a lokacin ganawar tasu, gwamnonin Arewa su 13 sun nemi afuwar Shugaba Buhari, kasancewa sun sanar da shi matsayin nasu ne bayan bullar labarin ta bayan fage.

Sun bayyana masa cewa sun yanke shawarar ce saboda a yi wa kowane bangare adalci a samu zaman lafiya a Najeriya.

Wannan sabon sa-toka-sa-katsi ya kunno kai ne a jajibirin gudanar da taron zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar mai mulki, bayan gwamnonin sun shaida wa Buhari cewa yankin Kudu ya kamata a bai wa takara.

Lalong ya ce gwamnonin za su yi wani zama a tsakaninsu ya yammacin ranar Litinin din.

Game da rashin ganin Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a wurin taron, Lalong ya ce Yayaya Bello ba ya cikin wadanda suka amince, hasali ba bai sanya hannu kan takardar bayan taron da gwamnonin suka fitar ba.

Da yake nasa tsokacin, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce Yahaya Bello yana da ’yancin bin ra’ayinsa.

Mahalarta zaman da gwamnonin suka yi da Buhari sun hada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebb; da Lalong da El-Rufai da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.

Sauran su ne Gwamna Abdullahi Sule, Nasarawa; Mohammed Inuwa Yahaya, Gombe; Mai Mala Buni, Yobe; Abubakar Sani Bello, Neja; Abdullahi Umar Ganduje, Kano; da Aminu Bello Masari, Katsina.

Akwai kuma Mohammed Abubakar Badaru, Jigawa da Abdurrahman Abdulrazaq, Kwara. Gwamnan Jihar Kogi kuma mai neman takara, Yahaya Bello bai halarci zaman ba.