Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce idan ba a kara kudin wutar lantarki nan da wata uku ba, za a rasa ta a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattawa da ke bincike kan karin kudin wutar da hukumar kula wutar lantarki (NERC) ta yi.
Kwamitin Majalisar Dattawa kan wutar lantarki ƙarƙashin jagorancin Sanata Enyinnaya Abaribe ya ki amincewa da karin farashin wutar.
Amma Adelabu ya ce, “Ina tabbatar muku cewa idan ba a kara kudin wutar lantarki a kasar nan ba, to za a daina samar da ita nan da wata uku, ko’ina zai kasance cikin duhu.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wahalar Fetur Ke Jigata ’Yan Najeriya
- Kun Kunyata Kanku Gwamnonin Arewa —Sule Lamiɗo
“Karin farashin zai taimaka wa aikin samar da wutar, mu ma ’yan Najeriya ne, muna jin yadda kowa yake ji”.
Ya bayyana cewa, “Gwamnati na buƙatar kashe Dala biliyan 10 a kowace shekara har tsawon shekaru 10 idan ana son a gyara masamar wutar lantarki.
“Wannan shi ne abin da ake bukata, kuma zancen gaskiya shi ne gwamnati ba za ta iya ba, dole mu yi abin da za mu iya domin janyo masu sanya jari su yarda da cewa za su ci riba idan suka saka kuɗinsu.”
Ya ce karin farashin wutar ga waɗanda ke tsarin band A har ya fara janyo hankalin masu zuba jari, sun fara nuna sha’awarsu.
Ya kuma ce gwamnati ba ta da niyyar bayar da tallafi a harkar lantarki, wanda hakan ne ya tilasta wa ɓangaren neman hanyar yin mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Najeriya ba ta tsunduma cikin duhu ba.
Sanata Simon Lalong da Sanata Adamu Aliero, sun ce ba a tuntubi ’yan Najeriya ko wakilansu ba kafin a kara kudin.
Suka kara da cewa, da an samar tallafi ga ’yan kasar domin rage raɗaɗin wannan ƙarin.
Sanata Abaribe, ya ce, “Abin da ’yan Najeriya ke so shi ne mafita mai ɗorewa a fannin”.
Ya kuma yi Allah wadai da rashin bayyanar da wani kamfani mai suna “ZIGLAKS” a gaban kwamitin.
Abaribe ya ce kamfanin ya karya yarjejeniyar samar da mitoci ga ’yan Najeriya, bayan da kamfanin ya karbi kusan Naira biliyan 32 a cikin shekaru 20 a Najeriya.
Sauran masu ruwa da tsaki da suka gabatar da jawabai a zaman binciken su ne: Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC), Kungiyar Masu Samar da Wutar Lantarki ta Najeriya (NAN), Hukumar Samar da Wutar Lantarki (Gencos), Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) da dai sauransu.