Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya ta naɗa Sheikh Dokta Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta.
Naɗin bajimin malamin na zuwa ne bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Jihar Osun.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shugabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.
Dokta Bashir sha-kundum ne a fagen ilimin shari’a da harkokin kuɗi da kasuwanci bisa tafarkin addinin Islama.
Ya yi digirin digirgir a fannin Hadisi da ilimin addinin Islama a Jami’ar Musulunci ta Madinah.
Kazalika, Dokta Bashir ya yi aiki kwamitoci daban-daban da harkokin kuɗi da Shari’ar Musulunci a nan gida da ƙetare ciki har da kwamitin mashawarta a Bankin Stanbic IBTC da da Majalisar Ƙwararru kan harkokin banki a tsarin addinin Islama da kuma Babban Bankin Nijeriya CBN.