Hukumomi a birnin Dnipro da ke kasar Ukraine sun haka kaburbura 600 saboda shirya wa cutar coronavirus da ke hallaka jama’a a duniya.
Hukumomin birnin zuwa yanzu sun ce, mutum 13 aka tabbatar na dauke da cutar, inda har yanzu babu wanda ya rasu.
Shugaban Karamar Hukumar Dnipro mai yawan jama’a kusan miliyan daya, Mista Borys Filatob, ya ce sun dauki matakai masu tsauri saboda firgita jama’ar birnin kan matakan da ya kamata su dauka don kauce wa kamuwa da cutar.
Mista Borys Filatob ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, suna shirye-shiryen ko- ta-kwana inda ya ce, an haka kaburbura 600 saboda jiran abin da ka iya faruwa.
“Muna shirin ne saboda halin ko-ta-kwana. Ba 400 ba, kaburbura 600 muka tona a makabartar birnin saboda binne wadanda ka iya rasuwa a lamarin.
An sayo jakunkunan sanya gawarwaki dubu daya saboda ajiyar gawarwakin mutane,” inji shi.
Kakakin Shugaban, Yulia Bitbitska, ta tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, hukumomin birnin sun tona Kaburbura 615 da samar da jakunkuna ajiye gawarwaki 2000 saboda shirya wa mutuwa a dalilin cutar coronavirus.
Yulia, ta ce an haramta binciken likitoci a kan duk wanda ya mutu a dalilin cutar ta coronavirus . Ba a nan ta tsaya ba, ta wallafa hotunan jerin kaburburan da aka tona a makabartar.
Wadansu mutane sun soki Shugaban kan matakin da yake dauka yayin da wadansu kuma suka yaba masa kan kokarin da ya yi na tilasta wa mutane zama a gida ta hanyar firgita su.
Filatob ya ce, “Wannan ba rudani na kawo ba, matakai ne na shirye- shirye. Ba ma fatar amfani da kaburburan da jakunkunan ajiyar gawarwakin.”