Kungiyar Malaman Jami’o’i t Kasa (ASUU) ta yi gargadin cewa idan ba a yi hankali ba, kwanan nan dokar bayar da rance ga dalibai za ta koro ’ya’yan talakawa daga makarantu.
A ranar Litinin ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan dokar da za ta ba daliban manyan makarantu masu karamin karfi damar su ci bashin karatu daga gwamnati, alabasshi su biya daga baya.
- Ganduje na son kotu ta hana EFCC bincikensa kan bidiyon Dala
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 100 a Borno
Mutane da dama dai sun yi ta jinjina wa Tinubun, inda suka ce ya cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe.
Sai dai yayin wata tattaunawarsa da Aminiya a ranar Laraba, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce dokar za ta iya kawo cikas ga dalibai masu karamin karfi da dama.
Ya ce babbar fargabarsu ita ce dokar za ta iya sa makarantu su kara samun kudaden karatu, wanda hakan zai shafi miliyoyin daliban da ke karatu a manyan makarantun Najeriya.
Ya ce, “A kasar da sama da mutum miliyan 133 talakawa ne kake son ka kara kudin makaranta? Hakan na da matukar illa.
“Ya kamata duk ’yan Najeriya su san da haka, kuma akwai yiwuwar a sake sanya hannu a kan wata dokar da za ta kara kudin makaranta.
“Idan dokar ta ce ta karin kudin makaranta ce, alhalin kuma ba a kara ba, mene ne mataki na gaba ke nan?” in ji shi.
Shugaban na ASUU ya ce dokar ba sabuwa ba ce, domin a baya ma lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sai da suka yake ta.
Sai dai ya ce har yanzu kungiyar babban samu nazartar dukkan kundin sabuwar dokar da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba, inda ya ce akwai bukatar fahimtarta sosai.