Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya bayyana takaicinsa ga abin da ya kira babban abin kunya bisa kin amincewa da kudurin dokar cin-gashin kai na Kananan hukumomin Najeriya da majalisun jihohi suka gaza aiwatar wa.
A yayin da yake karbar sakamakon kada kuri’un da majalisun jihohi suka yi a zaurukan majalisun a bisa gyaran dokar 1999 don ba su damar muhawara tare da neman amincewar su, shugaban majalisar ya ce har kawo yanzu majalisun bas u tabuka wani abin azo-a-gani ba. Amma duk da haka ya ce akwai sauran damar da ta rage na sake tura kudurin ga majalisun jihohin anan gaba, wadda amincewar tasu za ta yi tasirin da al’ummomin dake karkara zasu mori gajiyar dimokuradiyya.
Koda yake, Dogara ya yaba wa majalisun jihohin bisa kokarinsu na amincewa da kudurin dokar cin gashin-kai na majalisun jihohin, yana mai cewa amma yin hakan ba ya nuna wani kokari kasancewar abu ne da zai amfane su kai-tsaye, kila shi dalilin himmatuwar su wajen samar da dokar wacce majalisar tarrayya ta yi tsayin daka don ganin sun samu wannan ‘yancin na cin gashin-kansu ba tare an tsoma baki cikin sha’aninsu ba.
“Ya zama wajibi in yaba maku akan wannan, cewa akwai buqatar majalisun jihohi su samu damar cin gashin-kansu kai tsaye daga gwamnatin tarayya, amma ba shi ne kadai muradin da majalisar tarayya ke bukata ba. Don haka anan zan iya cewa ni a ra’ayina abin kunya ne musamman idan aka yi la’akari da kada kuri’ar amincewa da kudurin dokar kananan hukumomin kasar nan abu ne da aka jima ana dakon zuwansa don sakar wa kananan hukumomin mara ta yadda za su amfanin al’ummar karkara dake kusa da su, amma abin mamaki sai ga shi sun gaza yin hakan.”
“To amma mun ga irin karsashin da ku ke da ita, ba ta kai ga inda muka yi tsammani ba, wadda kila tsoro ne ya lullube ta, amma ta ya ya zababbe zai ji tsoron wani, idan ba don yadda wasu zaratanmu daga cikin maza da mata suka yi tsayin daka ba a can baya, da dimokuradiyyar ma da muke takama da ita a yau ba mu riske ta. A lokacin da William Wilberforce ya bayyana cewa dole ne a ‘yanta bayi su zama ‘yan jam’iyya, mafi yawan wadanda ke tare da turawan ne ke mallakar bayin, lamarin da ya haddasa boren tawaye kenan a lokacin,” in ji shi.
Hon. Dogara ya kara da cewa dukkan mizanin da ake dora majalisar tarayya a yau, muddin ya tsaya ne a tsakaninsu kadai, ba tare da samar da wata natijar da zata amfanar da al’ummarmu ta yau har ma da ta gobe ba, to ba yadda za a yi ace wannan ita ce dimokuradiyyar da muka jima muna dakon zuwanta a kasarmu.
Ya ci gaba da cewa, “Kamar dai kwatankwacin dokar cin gashin-kai na majalisun jihohi ne ya samu kin amincewa a karon farko, to babu shakka zai samu karbuwa a karo na biyu kamar dai yadda ya faru, to me zai hana tun da majalisun jihohi sun samu cikakken ‘yancin aikata dukkan abinda doka ta ba su iko, amma ace sun gaza samar wa kanananan hukumomi irin wannan ikon. Saboda dukkanmu mun san abin da ake nufi da ‘yanci.”
Sai kuma a karshe shugaban majalisar ya bukaci Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da ya baiwa wannan kuduri na kananan hukumomi kulawa ta musamman, don riskar da muradin al’ummar kasar nan wadanda baki dayanmu muke wakiltarsu a matakai daban-daban.