✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direbobin manyan motoci sun buɗe hanyar Abuja zuwa Lokoja

Bayanai da ke fitowa daga garin Abaji da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja na cewa direbobin manyan motoci sun buɗe hanyar bayan rufewar da…

Bayanai da ke fitowa daga garin Abaji da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja na cewa direbobin manyan motoci sun buɗe hanyar bayan rufewar da suka yi wadda ta janyo tsayawar sufuri.

Da farko dai direbobin sun rufe hanyar ne bayan da wasu sojoji da suka biyo hanyar suka lakaɗa wa wani direba dukan tsiya sakamakon kawo tsaiko ga tawagar jerin gwanon motocinsu.

Aminiya ta ruwaito cewa, sai da aka bai wa Shugaban Ƙungiyar Direbobin naira miliyan 1.6 gabanin buɗe hanyar da ta shafe aƙalla sa’o’i takwas a rufe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jagoran Bataliyar Sojin Gwagwalda mai muƙamin Laftanar-Kanar ne ya sasanta lamarin, inda direbobin suka buɗe hanyar da misalin ƙarfe 4:43 na yammacin wannan Alhamis ɗin.

Sai dai har yanzu hanyar ba ta warware ba a yayin da matafiya da suka maƙale a hanyar ke tafiyar hawainiya.

Wani da ya shaida faruwar lamarin, Zayyanu Bala, ya ce direbobin tankokin sun rufe hanyar ce tun misalin ƙarfe 9:00 na safe bayan da sojojin suka lakaɗa wa wani direban tanka duka tare da harbin tayoyi huɗu na motarsa.

Ya bayyana cewa sojojin sun fusata ne yayin da direban da abin ya shafa wanda ya taho daga Abuja ya ƙi bai wa jerin gwanon motocinsu hanya duk da jiniyar da suka riƙa yi.

“Ina zaune a bakin shagona na ga duk abin da ya faru yayin da sojojin suka sauko daga motocinsu suka fito da direban daga mota kuma suka lakaɗa masa duka.

“Bayan sun gama tara masa gajiya ne wani daga cikin sojojin ya zaro bindiga ya harbi tayoyi huɗu na motarsa.

Ya bayyana cewa wannan lamari ne ya fusata direbobin tankokin mai da na masu manyan motocin dakon kaya suka rufe hanyar mai hannu biyu.

Direban da abin ya shafa, Abdullahi Baba Ya’u wanda ya taso daga Abuja zai nufi Warri, ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne yayin da iso Abaji.

Ya ce cikin gaggawa ya sauka daga hanyar bayan da sojojin suka fara yi masa jiniya amma duk da haka wasu sojoji da ke kan babura a cikin tawagar sai da suka ci zarafinsa har ta kai shi gadon asibiti.

Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da sojoji da na Hukumar Kiyaye Haɗura FRSC sun yi ƙoƙarin shiga tsakani amma lamarin ya ci tura.

Tun da farko dai direbobin sun ce ba za su buɗe hanyar ba har sai gwamnati ta biya tayoyi huɗun da sojan ya harba.