✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direban Da Ya Kashe Masu Shara a Legas Ya Mika Kansa Ga ’Yan Sanda

Wani direba da ake zargi da take ma’aikatan shara har lahira a lokacin da suke tsaka da aiki a Legas ya mika kansa ga hukuma

Wani direba da ake zargi da take ma’aikatan shara har lahira a lokacin da suke tsaka da aiki a Legas ya mika kansa ga hukuma

Ana zargin zargin direban ya yi ajalin masu sharan ne bayan da ya taho da guje inda ya kade su a lokacin da suke tsaka da aikinsu a gefen babban titin Gbagada a ranar Litinin.

Kakakin ’yan sanda a jihar, Benjamin Huneyin, ya tabbatar cewa direban da ya mika kansa ga runduar yana nan a hannunsu.

Amma jami’in ya ce “ abun da ya faru ba kisa ba ne hadari ne, kuma za mu gurfanar da shi gaban kotu bisa zargin kisan kai, amma ba na ganganci ba”

A baya dai an ruwaito cewa, direban ya kade ma’aikatan sharar su biyu, suka mutu nan take, shi kuma ya tsere ya bar motar sa a wajen da abin ya faru.

Ana zargin hakan ta faru ne a bayan ya taho a guje da nufin tsere wa jami’an kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar, wadanda suka biyo shi a baya.

Sai dai ma’aikatar sufiri ta jihar ta ce babu wani jami’in ta da ke da hannu a faruwar al’amarin, ‘amma bayan binciken ’yan sanda, idan akwai ma’aikacinmu da ke da hannu za mu hukunta shi daidai da yadda doka ta ce.