✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direba zai shafe wata daya a kurkuku saboda satar taliya

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan samun shi daga laifin satar katan 14 na taliyar

Wata kotun majistare da ke zamanta a Otta a Jihar Ogun, ta aike da wani matashi mai shekara 21 gidan kurkuku, saboda satar katan 14 na taliya.

Kotun dai ta sami matashin, mai suna Kenneth Divine, da laifin satar kayan wadanda kimarsu ta kai kusan N48,000.

Tun da farko dai ’yan sanda sun zarge shi tare da wani mai suna Joel Olawole mai shekara 34 da laifukan aikata sata da kuma hadin baki.

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a A.O Adeyemi, ta yanke wa matashin hukuncin wata daya a gidan kaso bayan ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, ko kuma ya biya tarar N10,000.

Sai dai kuma alkalin ta umarci Kenneth ya biya mai kara N48,300 kudin kayan nasa.

Shi kuwa a nasa bangaren, Joel an ba da belinsa a kan kudi N50,000 da mutum daya da zai tsaya masa, duk da yake ya musanta aikata laifin.

Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Insfekta E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa Kenneth da Joel da wasu da suka tsere sun aikata laifin ne ranar 29 ga watan Maris, 2022 a yankin Oju-Ore da ke Otta.

Dan sandan ya ce sun sace katan 14 na taliyar Indomie da kudinsu ya kai N48,000 mallakin Balogun Ayokunle.

Ya ce laifin ya saba da tanade-tanaden sassa na 390(9) da na 516 na Kundin Manyan Laifuffuka na Jihar Ogun na shekarar 2006.

Daga nan sai ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 13 ga watan Mayu mai zuwa don ci gaba da sauraron karar (NAN)