A safiyar ranar Talata ne wani direban mota ya cika bujensa da iska bayan ya kade wata mata yayin da ta ke kokarin tsallaka titi, kuma daga bisani ta mutu.
Wani wanda ya ganewa idonsa Mista Uche Onah ya shaidawa Aminiya cewa rashin kula ya yi tasiri wajen aukuwar wannan tsautsayi yayin da matar ba ta duba da kyau ba gabanin tsallaka titin.
- Hatsarin babbar mota ya lakume rayuka 2 a Anambra
- An kama makauniyar karya a Anambra
- An gano budurwar da aka sace a Abuja a Anambra
- An gano masana’antar jarirai a Anambra
Mista Onah ya ce motar tana tsakar tsala gudu ne yayin da matar ta tsallaka, kuma direban bai sassauta ba wajen bi ta kanta.
Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) reshen jihar, Kamal Musa ya tabbatar da faruwar hadarin inda ya ce direban take ya tsere.
A cewarsa take aka tafi da ita zuwa asibitin Tronoto dake Onitsha, wanda a nan ne ajali ya katse mata hanzari.
Kwamandan hukumar jihar Anambra, Andrew Kumapayi ya jajanta wa iyalan matar, sannan ya ja hankali masu tafiya a kasa da suke amfani da gada yayin tsallaka titi.
Sannan ya yi kira da cewa mutane su rika tsallaka titi a lokacin danja ta tsayar da ababen hawa masu zirga-zirga babu kakkauta wa.
Kazalika, ya ja kunnen masu gudun da ya wuce kima a yayin da suke tuki.