✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Diphtheria: Najeriya Za ta dawo dokar sanya takunkumi

Jihar Kano ke da kashi 86 na wadanda suka kamu da cutar Diphtheria mai sarke numfashi

Gwamnatin Tarayya ta bukaci johihi su dawo da dokar sanya takunkumi da nufi dakile yaduwar cutar mashako ta Diphtheria.

Ma’aikatar Lafiya ta ta bukaci hakan ne da cewa matakin zai rage yaduwar cutar, wadda a halin yanzu aka samu yaduwartaa jihohi 19, inda jihar Kano ke kan gaba da kashi 86 na masu cutar.

Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dokta Faisal Shuaib, ya bayyana cewa hadarin cutar da yadda take yaduwa, na kama da COVID-19, don haka ya jaddada muhimmancin yin allurar riga kafinta da kuma matakan kariya kamar yadda aka yi a lokacin COVID-19.

“Diphtheria cuta ce da ke bin iska kamar COVID-19, wadda za a rage shakar iska mai kwayarta ta hanyar sanya takunkumi, wanke hannu, da kuma nisantar masu ita, amma ba tare da tsangwamar su ba.”

“Annobar wadda ta fi kama yara ’yan kasa da shekaru 15, inda kawo yanzu mutum 8,406 suka harbu da ita a kananan hukumomi 114 na wasu jihoi 19 da 114,” in ji shi a taron kwamitin yaki da cutar da kasa da ya gudana a Abuja.

Ya bayyana cewa, “Jihar Kano na masu cutar da mutum 7,188, sai Yobe, 775; Katsina, 232; Borno, 118; Jigawa, 23; Bauchi, 20; Kaduna 17; Legos, 8; Abuja, 6; Gombe, 5; Osun, 3; Sakkwato, 3; Neja, 2; Cross River, 1; Enugu, 1; Imo, 1; Nasarawa, 1; Zamfara, 1; and Kebbi, 1.”

A yayin taron, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Hukumar Dikile Yaduwar Cututtuka (NCDC) suke jagoranta, Dokta Faisal ya ce, “Diphtheria cuta ce da ke bin iska kamar COVID-19, wadda za a rage shakar iska mai kwayarta ta hanyar sanya takunkumi, wanke hannu, da kuma nisantar masu ita, amma ba tare da tsangwamar su ba.”

Ya yaba da irin hadin kan da aka samu tsakanin duk matakan gwamanti da sauran masu ruwa da tsaki da hukumomin kasa da kasa wajen tunkarar annobar.

“Babbar mafita ita ce riga kafi sau biyu, wanda yanzu aka tsara a yankunan da cutar ta fi kamari kamar Kano, kuma ina kira ga jama’a da su ba da hadin kai,” in ji shi.

Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Alexander Chimbaru ya jaddada muhimmacin samun goyon bayan sarakunan gargajiya da shugabannin addini da sauransu wajen samun nasarar  aikin yin rigakafin cutar diphheria.

%d bloggers like this: