✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diloli sun karya farashin fulawa a Kano

Za mu rika sayar wa masu burodi fulawa kai tsaye ta hannun kungiyoyinsu.

Dilolin fulawa a manyan kasuwannin Kano sun ce suna aiki ba dare ba rana domin magance matsalar hauhawar farashin fulawa da sauran kayayyaki a jihar.

Junaidu Muhammad Zakari, shugaban kungiyar ’yan Kasuwar Singer, ya bayyana hakan jim kadan bayan wata ganawa da Hukumar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa (PCACC) a ranar Juma’a.

Aminiya ta ruwaito cewa kayyakin abincin musamman fulawa sun yi tashin gwauron zabi a Jihar Kano bayan da gwamnati ta sassauta dokar hana fita da ta ƙaƙaba a sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa da rikide zuwa tarzoma a farkon watan Agusta.

Da yake zantawa da Aminiya, Zakari ya ce wannan tsadar kayayyaki mai tayar da hankali da ake gani ta faru ne bayan bai wa jama’a damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum da aka yi a ranar 6 ga watan Agusta.

“Ko shakka babu, mun tattauna kuma mun cimma matsaya da gwamnati.

“Duba da cewa masu gidajen burodi ne ke matuƙar buƙatar fulawa, su ma mun zauna da su domin yi wa tufkar hanci, amma dai wannan dabi’a ta tsawwala farashi da wasu ’yan kasuwarmu ke yi abin Allah wadai ne.

“A yanzu mun cimma matsayar cewa za mu riƙa sayar musu da fulawar kai tsaye ta hannun wakilan kungiyoyinsu [masu gidajen burodi]a kan farashi mai rahusa.

“Mun shaida musu cewa muna da fulawa a ƙasa kuma mun riga mun ba su, wasu kuma na nan tafe tare ba su tabbacin za mu sayar musu da fulawar kai tsaye domin magance matsalar faɗawa hannun masu ƙara farashi.

“Za mu ci gaba da hakan har sai farashin kayan sun faɗi a yayin da muke ba su tabbacin ci gaba da goyon baya a kasuwancinsu.

“Haka nan muna sa ran nan ba da jimawa ba za mu riƙa sayar da fulawar ga daidaikun mutane a kan farashi mai sauƙi ta yadda kowa zai samu fulawa a farashi mai rahusa.”

A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa (PCACC), Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana cewa, a kokarin da suke yi na ganin jama’a sun samu saukin rayuwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.

“Kowa ya san akwai hauhawar farashin kayayyaki da aka ƙirƙiro babu dalili a jihar. A fulawa kaɗai an samu ƙarin Naira 20,000.

“Saboda wannan dalili ne gwamna ya ba da umarnin a gaggauta magance matsalar a yayin da wasu masu gidajen burodi sun fara watsi da sana’ar suna neman shiga yajin aiki.

“A yau mun gana da ‘yan kasuwar kuma mun cimma matsaya da dilolin fulawa da sauransu, kuma sun amince tare da ba mu tabbacin za a ga sauyi a lamarin,” in ji Muhuyi.