✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diego Simeone ya tsawaita kwantaraginsa a Atletico Madrid

Simeone zai ci gaba da kocin Atletico Madrid har zuwa 2024.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Diego Simeone ya tsawaita kwantaraginsa a kungiyar har zuwa kakar wasanni ta 2024.

Kungiyar ta amince wajen sabunta zaman nasa ne saboda bajinta da ya yi wajen kai ta ga gaci har ta lashe gasar La-Liga.

  1. Allah Ya yi wa Sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu rasuwa
  2. Za a maida gidajen kallo makarantun Islamiyya a Katsina

Simeone ya karbi ragamar kocin Atletico Madrid ne tun a shekarar 2011, inda ya lashe kofi takwas.

Ya lashe gasar Laliga, gasar Europa, Copa del Rey da UEFA Super Cup tun bayan zama kocin kungiyar.

Kazalika, Simeone ya kuma jagoranci kungiyar a wasanni 527, inda suka yi rashin nasara a kaso 16 cikin 100 na wasannin da suka fafata.