Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin.
Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata-ɓurza tsakanin Real Sociedad da Osasuna.
- Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya?
- Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu
Ana sa ran buga wasannin da za a gudanar ranar 5 ga watan Fabrairu.
A jadawalin ya bayar da damar sake buga El Clasico wato karawar hamayya tsakanin Real da Barcelona a wasan ƙarshe da suka daɗe ba su haɗu a gasar tsawon shekaru.
An haɗu a wasan karshe a Copa del Rey karawar El Clasico sau 18, Real ce ta yi nasara 11 daga ciki, wasan baya bayan nan da suka kara shi ne a 2014. Kuma Real Madrid ce ta lashe kofin da cin 2-1 a wasan da aka yi a Valencia.
Sai dai a kakar bana, Barcelona ta caskara Real Madrid karo biyu a baya, wadda ta fara cin 4-0 a Santiago Bernabeu cikin watan Oktoban 2024.
Sai kuma Barcelona ta lashe Spanish Super Cup na bana a kan Real Madrid da cin 5-2 a Saudi Arabia a makon jiya.
Real Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da maki 46, sai Atletico Madrid ta biyu da kuma Barcelona ta uku da tazarar maki makwai tsakani da Real.
Barcelona za ta je gidan Valencia a Copa del Rey zagayen kwata fainal, kamar yadda aka raba jaddawali ranar Litinin.
Barcelona ta kawo wannan matakin, sakamakon nasara a kan Real Betis 5-1 ranar Laraba 15 ga watan Janairu a zagayen ‘yan 16.
Ita kuwa Valencia zuwa ta yi ta doke Ourense 2-0 ranar Talata 14 ga watan Janairu.
Valencia da Barcelona za su fuskanci juna a zagayen ’yan takwas ranar Laraba 5 ga watan Fabrairu a filin wasa da ake kira Mestalla.
Jadawalin kwata fainal a Copa del Rey:
Leganes da Real Madrid
Atlético Madrid da Getafe
Real Sociedad da Osasuna
Valencia da Barcelona