Jaridar Sport ta ruwaito cewa dan wasan gaban Barcelona da Netherlands Memphis Depay na son komawa Manchester United, shekaru shida bayan ya bar Old Trafford.
Manchester City kuwa ta shirya karfafa tsakiyarta badi, kuma dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham na cikin wadanda za ta yi amfani da su wurin cimma burinta.(ESPN).
- Bayan kai ruwa rana, Majalisar Amurka ta yi Shugaba
- Hamshakan masu kudin duniya sun tafka asarar tiriliyan N518 a 2022
Tuni kungiyoyin Madrid da Liverpool suka nuna sha’awar sayen matashin mai shekaru 19, kuma Dortmund na son ya tabbatar mata idan yana son ci gaba da wasa a kungiyar a kaka ta gaba.(90min).
Ita kuma Chelsea na ci gaba da tattaunawa da Shakhtar Donetsk kan dan wasan gabanta Mykhailo Mudryk.
Haka ma kungiyar ta Stamford Bridge na magana da Benfica kan Enzo Fernandez, kuma tuni ta kammala sayen Andrey Santos daga Vasco da Gama, in ji Metro.
A nan kuma jaridar Sun, ta ruwaito cewa Chelsea da Arsenal na rige-rigen sayen Mudyryk na Shakhtar Donetsk.
To amma Telegraph ta ce akwai yiwuwar Arsenal ta fi mayar da hankali wurin kawo Joao Felix na Atletico Madrid.
Kocin Gunners din Mikel Arteta na kokarin ganin kungiyar ta sawo Mudryk da Felix a watan Janairun nan, in ji Mirror.
Manchester United kuwa ta kammala yarjejeniyar dauko dan wasan gaban Kamaru da Al Nassr ta Saudiyya, Vincent Boubakar.(OKAZ, via TALKSPORT)
Juventus da Barcelona kuwa sun nuna sha’awar daukar Wilfred Zaha na Ivory Coast, wanda kwantiraginsa ke shirin karewa da Crystal Palace. (Evening Standard).
A Ingila kuwa Liverpool da Chelsea na rige-rigen sayen dan wasan tsakiyar Brighton Moises Caicedo, a cewar Sky Sports.
A daya waje kuwa Chelsea ta nuna sha’awar raba Borussia Monchengladbach da dan wasan gabanta Marcus Thuram, wanda dan Faransa ne, kamar yadda jaridar Foot Mercato ta ruwaito.
Kocin West Ham David Moyes na fuskantar mako biyu masu zafi, inda zai kara da Wolves da Everton, wasannin da za su bayyana makomarsa a kungiyar.
Tottenham Hotspur da Juventus na rige-rigen kulla yarjejeniya da tsohon kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane.
Spurs dai na son maye gurbin Antonio Conte muddin bai tsawaita kwantaragin zamansa a kungiyar ba wanda zai kare a karshen kakar nan. Fichajes
Ita ma kungiyar da ke Turin na zawarcin Zidane din domin maye gurbin Massimiliano Allegri muddin ta samu dama. Goal