Tsohon dan wasan Ingila, David Beckham, ya bai wa tsohon mai tsaron ragar Manchester United, David de Gea damar ya koma wa kungiyarsa ta Inter Miami da ke Amurka.
A halin yanzu dai De Gea ba shi da kwantiragin kowacce kungiya a kansa tun bayan da United ta ki sabunta yarjejeniyarsa, inda ta dauko Andre Onana a madadinsa.
- PDP ta lashe zaben duk kananan hukumomi 16 a Taraba
- Super Eagles ta kara tuntube a wasan neman gurbin Gasar Kofin Duniya
Jaridar Sun ta ruwaito cewa David de Gea ya ki amincewa da tayin albashin fam 500,000 duk mako da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, inda zai hade da abokin taka ledarsa a kungiyar Manchester United, Cristiano Ronaldo.
De Gea mai shekara 33 a duniya, ya ki zuwa wasu kungiyoyi da suka nuna sha’awar daukar sa kamar Inter Milan, Valencia, Real Betis, har ma da wasu kungiyoyin Saudiyya.
Idan dai mai tsaron ragar ya yarda da komawa Inter Miami, zai ci gaba da taka leda tare da Lionel Messi, da ’yan kasarsa ta Sifaniya, Jordi Alba da Sergio Busquet, wadanda suka koma kungiyar a kakar da ta gabata.