✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Super Eagles ta kara tuntube a wasan neman gurbin Gasar Kofin Duniya

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Najeriya ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.

Tawagar Kwallon Kafar Najeriya ta Super Eagles ta sake yin tuntube a wasannin neman tikitin zuwa Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Super Eagles ta yi tuntuben ne bayan ta tashi 1-1 tsakaninta da ta Zimbabwe ranar Lahadi a wasan da aka buga a Rwanda.

Tun da farko dai, dan wasan Zimbabwe Walter Musona ne ya zura kwallon farko a minti na 26 da fara wasan ta hanyar bugun tazara.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Najeriya ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.

Wasa na biyu kenan da Najeriya ta tashi 1-1 a karawar cikin rukuni na uku, bayan da ta yi kunnen doki da Lesotho a Uyo ranar Alhamis.

Ita kanta Zimbabwe ta tashi wasan farko a cikin rukuni da Rwanda ba ci ranar Laraba.

Zimbabwe na buga wasanninta a Rwanda saboda ba ta da filin wasa mai darajar da za a buga wasannin.

Bayan wasa 2 a rukunin C, Najeriya na da maki 2 kacal a yayin da take shirin karɓar baƙuncin Afirka ta Kudu a wasan gaba.

%d bloggers like this: