✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba na kewar barin kujerar shugabancin Najeriya — Buhari

Ina jin likita na ne kaɗai zai iya ba da hakikanin amsa a kan koshin lafiyata.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce kawo yanzu ko kadan ba ya kewar barin kujerar shugabancin Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Gidan Talabijin na Kasa NTA.

Bayanai sun ce wannan ita ce hirarsa ta farko tun bayan kammala wa’adin mulkinsa na karshe a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Da yake amsa tambayar abin da ya fi kewa a yanzu bayan barin kujerar shugabancin Najeriya, Buhari ya ce “ba na jin akwai wani abin da nake kewa a yanzu.”

Cikin sanarwar da NTA ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a saki cikakkiyar hirar da aka yi da Buharin da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Litinin.

Tun ba yanzu ba dai Buhari ya sha cewa ba zai yi kewar barin kujerar shugabancin Najeriya ba, saboda duk abin da yake yi ba a gani.

A watan Disambar 2022 ne tsohon Shugaban Kasar ya ce yana yi wa ’yan Najeriya iyaka kokarinsa amma ba a yabawa.

Daga shekarar 2015 zuwa 2021, Buhari ya shafe kwanaki 171 a Birtaniya wajen neman lafiya, inda a shekarar 2017 kaɗai, ya shafe kwanaki 152 yana neman lafiya.

“Ina jin likita na ne kaɗai zai iya ba da hakikanin amsa a kan koshin lafiyata,” a cewar Buharin da aka tambaye shi kan rashin lafiyar da ya yi fama da ita.