Golan Sifaniya David de Gea, ya sanar da cewa zai bar Manchester United bayan shafe shekara 12 a kungiyar.
A cewarsa, “lokaci ya yi da ya kamata ya fuskanci sabon kalubalen rayuwa”.
- Bazamfariya ta yi tsintuwar kusan Naira miliyan 60 a Saudiyya
- Tinubu zai halarci taron ECOWAS a Guinea-Bissau
Golan mai shekara 32 wanda ya ci kyautar safar hannu ta gwal a Gasar Firimiya ta bara a matsayin wanda ya fi tare kwallaye a kakar bara, ya sha caccaka kan manyan kurakuran da ya rinka tafkawa a makon karshe na gasar.
Kwanitraginsa da Manchester United ya zo karshe ne a watan Yuni, inda ba a cimma wata yarjejeniya ta sake sabunta ta ba duk da tattaunawar da aka rinka yi a cikin kakar.
A wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta, De Ge ya gode wa masoyansa na United kan irin goyon bayan da suka ba shi.
Sa’annan ya ce Manchester United za ta ci gaba da zama a cikin zuciyarsa.
A lokacin da kwantiraginsa ya kare a Juma’ar da ta gabata, United ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dan wasan na Sifaniya.
De Gea wanda a kakar da ta gabata ya goge tarihin Peter Schmeichel a matsayin mai tsaron raga mafi doka wasanni masu yawa ba tare da an zura masa kwallo ba, ya lashe kyautar tauraron dan wasa da kuma kyautar dan wasa mafi soyuwa a wajen magoya baya tsawon shekaru 4 a jere.
De Gea ya soma taka leda a Atletico Madrid, amma Manchester United ta siye shi kan fam miliyan 18.9 a 2011.
De Gea wanda Sir Alex Ferguson ya sayo a shekarar 2011 ya dokawa United wasanni 545 ciki har da 190 da ba a iya zura masa kwallo ba.
Tafiyar De Gea na nuna cewa kaf cikin tawagar ta yanzu babu ko da dan wasa 1 da ya lashe kofin firimiya a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013 wadda ke matsayin kaka ta karshe karkashin jagorancin Ferguson.
A tsawon lokacin da ya shafe ya na taka leda De Gea ya kuma lashe kofunan FA 2016 da League Cup kana Europa.
Ana rade-radin cewa United na shirin maye gurbin De Gea da golan Milan, Andre Onana wanda Erik ten Hag ya horas a Ajax.