Fitaccen dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Kevin De Bruyne, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar Firimiyar Ingila a karo na biyu.
Dan wasan mai shekara 29, ya kafa tarihi wajen lashe kyautar kungiyar kwararrun ’yan wasan Ingila ajin mazaa karo na biyu a jere kwatankwacin tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa a lokacin da yake Manchester United.
De Bruyne wanda dan asalin kasar Belgium ne, ya zura kwallaye shida a bana tare da taimakawa wajen zura kwallaye 12 a raga.
Dan wasan ya taka muhimmiyar rawa inda taimaka wa kungiyarsa ta Manchester City wajen lashe gasar Firimiyar Ingila a bana.
Sai dai kungiyar tasa ta yi rashin nasara a hannun Chelsea ta ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai.