✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

De Bruyne ya sabunta kwantaraginsa a Manchester City

Dan wasan ya zamo jigo a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City

Dan wasan Manchester City na kasar Belgium, Kevin De Bruyne, ya sabunta kwantaraginsa na ci gaba da zama a kungiyar har zuwa 2025.

De Bruyne ya sabunta kwantaraginsa ne bayan samun nasarar da Manchester City ta yi a kan kungiyar Dortmund a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Dan wansan ya lashe kofin Firimiya biyu da FA Cup da League Cup hudu tun bayan zuwansa City daga Wolfsburg a shekarar 2015.

Yana kuma daga cikin manyan ’yan wasan da Manchester City ke ji da su.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ita ce ta daya a kan teburin Firimiya da tazarar maki 14 tsakaninta da Manchester United da take ta biyu a teburin.