Daya daga cikin ’yan makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) Birnin Yauri da ke jihar Kebbi, wacce ’yan bindiga suka sace a 2021 ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa dalibar mai shekara 16 na daya daga cikin ’yan mata 11 da har yanzu ba a sako ba tun bayan sace sama da su 100 da malamansu takwas, ranar 17 ga watan Yunin 2021.
- Mun yi wa ’yan Najeriya miliyan 65.5 rigakafin COVID-19 – Gwamnati
- Jiragen yakin Amurka 2 sun yi taho-mu-gama a sararin samaniya
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa kafar cewa dalibar, wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance sunanta ba, ta haifi da namiji ne a sansanin ’yan bindigar.
Majiyar ta shaida wa kafar cewa iyayen yaran na cike da damuwa kasancewar har yanzu an ki sakin ’ya’yan nasu, duk kuwa da biyan kudin fansa da musayar fursunonin da aka yi da ’yan ta’addan.
Majiyar ta ce, “Lokacin da gwamnati, musamman Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ta ce sam ba za ta tattauna da ’yan bindigar ba da ke bukatar biyan fansa ba, sai iyalan yaran suka tattara taro da kwabo don karbo yaran nasu.
“Abin takaici ne matuka yadda ’yan bindigar suka karbi kudin fansa mai yawa sannan suka aurar da wasu daga cikin ’yan matan, amma suka ki su sako ragowar,” inji majiyar.
Idan dai za a iya tunawa, ’yan kwanaki kadan bayan sace daliban, jami’an tsaro sun sami nasarar ceto wasu daga cikin mutanen, yayin da wasu suka gudu cikin daji lokacin da ake kokarin kwashe su.
Kazalika, ’yan ta’addan sun kuma sako malami daya da dalibai 30.