Daya daga cikin manyan Sarakunan Jihar Oyo, mai martaba Aseyin na Iseyin, Oba Abdulganiyu Adekunle Salawudeen ya kwanta dama.
Marigayi basaraken mai shekaru 62 ya rasu ne a ranar Lahadi, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan da ke Ibadan bayan fama da rashin lafiya.
- ’Yan bindiga sun kashe direba, sun kwashe fasinjoji a hanyar Jibiya da rana tsaka
- Zan gina alkaryar nishadi a Osun – Zababben Gwamna Adeleke
Tsohon likitan dabbobi, Aseyin na Iseyin, ya zama Sarki a masarautar Iseyin ne a shekarar 2007.
Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar sa a ranar Lahadi.
Oba Abdulganiyu Adekunle Salawudeen dai yanzu ya shiga sahun manyan Sarakuna hudu da suka riga mu gidan gaskiya a Jihar Oyo da har yanzu ba a nada sababbin Sarakunan da za su gaji uku daga cikin su a masarautarsu ba.
Sarakunan da suka kwanta dama a baya-bayan nan a jihar sun hada da Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewunmi Ajagungbade da Alaafin na Oyo Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi da Asigangan na Igangan.