Gwamnatin Tarayya ta ce dawo da Shugaban Hukumar NHIS, Usman Yusuf da aka yi bakin aiki ba zai hana Hukumar EFCC ci gaba da bincikensa ba.
Ministan Labarai da Al’adu na qasa, Alhaji Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan sun kammala taron Majalisar Zantarwa wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Shi dai Usman Yusuf an dakatar da shi ne tun Yuni na bara bisa zargin cin hanci da rashawa a karkashin Minsitan Lafiya, Isaac Adewole, amma sai kwatsam aka dawo da shi bakin aiki.