Wani dattijo da ya haura shekara 80, Malam Abdullahi Ishai Gwabdi Ayu ya kasance mutumin da jama’a da dama ke mamakin yanayin rasuwarsa, inda wasu suke tunanin ko ba mutum ba ne.
Hakan ya biyo bayan gina gida da ya yi a wani dan tsibiri a tsakiyar Kogin Galma da ke Zariya a hanyar Jos inda yake zaune shi da iyalinsa kimanin shekara 50.
Kogin Galma shi ne ya fito daga garin Shika ya ratso ta Hanwa ya biyo ta Tudun Wadan Zariya inda har ya hadu da Kogin Kamacha sannan ya zarce ya ratsa tsoho da sabon Titin Jos sannan ya wuce har cikin garin Kaduna.
Gidan Malam Abdullahi na nan a tsakanin tsohuwar gada da sabuwar gadar Titin Jos ta bayan Unguwar kaya da ke Tudun Wadan Zariya.
Jama’a sun dade suna mamakin mutumin da ke zama a wannan wuri komai yawan ruwa. Domin idan damina ta yi nisa, gidan ma yakan shafe gaba daya, ya zama ba a ganinsa. Sai bayan ruwa ya yi sauki sannan a sake ganin gidan ya fito.
Malam Abdullahi Ishai Gwabdi dan kabilar Ayu ne da ya yi hijira daga garin Kafanchan na Jihar Kaduna zuwa garin Zariya, inda ya yi masauki a tsakiyar kogin, har ma ya gina gida a tsakiyar kogin.
‘Na zo Zariya ne don in Musulunta’
A zantawarsa da Aminiya, ya ce ba shi da wata sana’a da ta wuce su da farauta, sannan yana hadawa da aikin noma.
Ya ce ya zo Zariya de a 1972 da nufin ya Musulunta kuma ya samu ilimin addinin Musulunci, wanda kuma a cewarsa tuni ya cim ma burinsa.
Malam Abdullahi wanda jama’a suka fi yi wa lakabi da Sarkin Kogi ko Sarkin Ruwa, ya ce babu wanda ya taba nada shi a wadannan sarautu don haka ya fi so a kira shi da “Mai gida a cikin ruwa.”
“Lokacin da na zo Zariya, lokacin mulkin Sarki Muhammadu Aminu ne kuma a lokacin ina da ’ya’ya uku.
“A nan garin Zariya kuma na haifi ’ya’ya 19, yanzu haka ina da ’ya’ya 22. Kuma Allah cikin ikonSa, na samu arziki daidai gwargwado domin har na mallaki gidaje guda uku a garin Zariya,” in ji shi.
Dangane da yadda yake rayuwa da iyalinsa a tsakiyar wannan kogi, Malam Abdullahi ya ce a wannan gida suke zaune gaba dayansu, sai dai idan damina ta yi nisa kuma ruwa ya kawo sosai, yana kwashe su ya mayar da su Unguwar Gyallesu inda yake da wani gidan, domin su zauna a can.
Shi kuwa yakan dawo ya ci gaba da zama a wannan gida komai rani komai damina.
Da Aminiya ta tambaye shi ko ya taba haduwa da mutanen boye, ko wasu halittu da suka taba firgita shi, Malam Abdullahi Ishai ya ce suna haduwa da mutanen boye, amma babu wanda ke cutar da wani.
“Muna zaman lafiya da su. Kowa yana sha’aninsa ba tare da wani ya tsangwami wani ba.
“A tsawon shekarun nan 50 da na yi a cikin ruwa, ban taba ganin wani abu ko wata halitta da ta taba firgita ni ko ta ba ni tsoro ba.
“Sau daya ne, farkon lokacin da na zo na taba haduwa da wani maciji wanda ya so mu fafata da shi, amma daga bisani na ce masa ya tafi abin sa, in ba wata fitina yake so ba.
“Nan take kuwa ya kama hanyarsa ya tafi.
“To ni ban da wannan, ban taba ko sa-in-sa da wata halitta ba a wannan wuri,” in ji shi.
Mai gida a ruwan, ya ci gaba da cewa yana taimakon jama’a wajen tsamo gawar mutane wadanda ruwa ya ci su, in aka sanar da shi.
Ya ce ba zai iya tuna yawan gawarwakin da ya ciro ba domin yawansu sannan shi kadai yake wannan aiki ba tare da sa hannun ’ya’yansa ko mutanen gari ba.
Dangane da sirrin da yake amfani da shi wajen zama a wannan ruwa ba tare da tsangwama ba duk da ana zargin kogin da kasancewa matattarar ibilisai musamman yadda a duk shekara sai ruwan ya cinye mutane da dama, Malam Abdullahi ya ce shi ba ya da wani sirri illa karfin hali irin na maharba.
Aminiya ta gano cewa mutane sukan ziyarci mai gida a ruwan don neman magungunan sanyi da na wasu siddabaru.
Malam Abdullahi Ishai Gwabdi ya ce ba ya da sauran wani buri a duniya illa ya cika da imani.