✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dattijo ya nemi budurwa ta biya shi N50,000 saboda kin auren shi

Mutumin mai shekara 72 ya ce tun da dai ba kira bai ga abin da zai ci masa gawayi ba.

Wani tsoho mai shekara 72, Musa Abdullahi ya gurfanar da budurwarsa gaban kotu yana rokon a tilasta mata biyan sa kudaden da ya kashe mata tunda ta ki amincewa ta aure shi.

Musa ya roki kotun yankin Gwagwalda a Birnin Tarayya Abuja ta tilasta wa Rukayya Idris mai shekara 18 ta biya shi Naira 50,200 da ya kashe mata.

Ya ce tun da dai ba kira bai ga abin da zai ci masa gawayi ba.

Dattijon, ya shaida wa kotun cewa ya fara neman auren Rukayya ne tun a watan Yunin 2020 kuma a lokaci ta amince za ta aure shi amma daga bisani ta kekashe kasa ta ce allambaran.

Malam Musa ya ce daga watan Yuni zuwa Nuwamba ya kashe mata kimanin N50,200, wadanda yake rokon kotun da ta tilasta mata maido masa da su.

To sai dai mahaifin budurwar mai suna Idris Abdullahi wanda ya halrci zaman kotun tare da diyar tasa ya musanta ikirarin, inda ya ce N6,000 kawai ya sani ya taba ba shi wata rana da ya zo hira.

Ita ma Rukayyan ta ce ba ta san N50,200 da yake ikirarin kashe mata ba, in banda jimlar wata N8,000 da ya kashe mata a lokuta daban-daban.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Adamu Isah ya dage sauraron karar zuwa 25 ga watan Nuwamba domin ba wa mai karar damar gabatar da shaidun kudaden da ya ce ya kashe.