✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood ta yi martani kan hana amfani da kakin ’yan sanda a fim

Aminu Saira da Aminu S. Bono sun ce ba za ta sabu bindiga a ruwa ba.

Wasu daga cikin Daraktoci a Masana’antar Shirya Fina-Finan Hausa ta Kano da aka fi sani da Kannywood, sun mayar da martani game da dokar hana amfani da kakin ‘yan sanda a cikin fina-finai da Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bayar.

Usman Baba, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja mai dauke da sa hannun kakakin ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da cewa an haramta wa masu shirya fina-finai da masu barkwanci yin amfani da kakin ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu ba tare da izini ga ‘yan sanda ba kamar yadda doka ta tanadar ba.

Sanarwar ta kara da cewa ’yan fim su daina yi wa rundunar ‘yan sandan Najeriya kallon banza ko kuma ba’a a cikin ayyukansu.

Wani fitaccen darakta a Kannywood, Aminu Saira, ya shaida wa sashen Hausa na BBC, cewa za su yi nazarin umarnin idan ya dace da dokokin Najeriya sannan su bi shi.

Saira ya ci gaba da cewa, idan binciken da suka gudanar ya nuna cewa ba su saba wa kowace dokar kasa ba, to za su hada kai da Nollywood domin kalubalantar umarnin a gaban kotu.

Ya ce, “’Yan sanda da masu shirya fina-finai duk suna karkashin dokokin Najeriya ne, duk mutanen da ke zaune a Najeriya dole ne su yi biyayya ga dokokin Najeriya.

“Don haka idan har dokar Najeriya ta haramta amfani da kakin ‘yan sanda a fim, dole ne mu kiyaye, mu mutunta dokar kasa, ba mu da wata hanya.

“Amma idan Dokar ba ta hana ba, to za mu hada kai tare da Nollywood don neman masaniya ta hanyar shari’a kan hukuncin amfani da kakin ‘yan sanda.”

A cewarsa, Kannywood ta jima da fara neman izini kan amfani da abubuwan da suka shafi ‘yan sanda a cikin fina-finansu daga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano.

Ya ce saboda wasu abubuwan da suka faru a baya, an umarce su da su nemi izini a duk wata rawa da ta shafi ’yan sanda a cikin fina-finansu.

“A yanzu haka akwai wani kamfani da ‘yan sanda suka ba da takardar shaida wanda ya kware wajen sarrafa duk wani abu da ya shafi ‘yan sanda kamar bindigu, kaki a sauransu da za a yi amfani da su a fim. Sai ka tura musu takardar fim din sun duba, sannan su ba da izini,” a cewar daraktan.

Shi ma darakta Aminu S. Bono, wanda ya ce Sufeton ‘yan sanda bai tuntubi masu ruwa da tsaki ba, ya bayar da hujjar cewa a duk duniya ba zai yiwu a hana amfani da kaya irin na su lauyoyi, sojoji ko likitoci a fina-finai ba saboda kawai suna kwaikwayon hakikanin abin da ke faruwa ga al’umma ne.

Ya kara da cewa a duk fina-finansu, suna samun izini daga ‘yan sanda kafin fara amfani da wani abu da ya shafe su.

“Mu a jihar Kano akwai sashen da ke kula da irin wadannan abubuwa a karkashin kakakin ‘yan sanda, ‘yan sanda a wasu lokutan suna ziyartar wuraren da muke daukar fim, su yi mana jagora kan yadda za mu yi abubuwan da suka shafi aikinsu.

“Mun yi fina-finan da suka shafi ‘yan sanda kai tsaye inda muka yi amfani da ofisoshin ‘yan sandan Kano, a fina-finai kamar ‘Kwana Casa’in da ‘Barazana’, mun yi aiki kafada da kafada da ‘yan sanda.”

Ya kuma bayyana cewa ‘yan sanda suna da wakilci a Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, inda ake tace fina-finan Kannywood kafin su fita kasuwa.

Ya ce har yanzu Sufeton ‘yan sanda na iya yin duba ga wannan doka tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don nemo mafita.