Darajar takardar kudin Ruble na kasar Rasha ta kai matsayi mafi girma da ba ta taba kai wa ba a cikin shekaru bakwai a kan kudin Yuro.
Kudin na Ruble wanda tsadar man fetur da iskar gas ta sa ya yi tashin goron zabi a kasuwannin hada-hada na kudi, ya haura da sama da kishi 20 cikin dari a gaban kudin Yuro fiye da lokacin da aka soma yin yakin.
- Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a Afirka ta Kudu
- Buhari ya gana da ’yan uwan wadanda suka rasu a iftila’in Kano
A halin da ake ciki kamfanoni da yawa na Turan ya zame musu dole kanwar naki, wajen bin umarnin Putin na yin cinikayyar a Rashar da kudin Rubel.
Kudin Rashan shi ne kudin duniya wanda ya fi samun ci gaba fiye da kowanne tun farkon shekara.