✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dankarami: Dan bindigar Zamfara da ke rawa da bazar mahaifinsa

Shekarun Dankarami 30 da wani abu, amma yana jagorantar ’yan bindiga 500.

Al’ummomin Jihar Zamfara da dama kamar na Gidan Jaja da sauransu a Karamar Hukumar Zurmi da wadansu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina suna cikin halin tsaka-mai-wuya sakamakon fada wa tarkon wani kasurgumin dan bindiga mai suna Dankarami, wanda aka fi sani da Small.

Dajin Jaja da ke makwabtaka da yankin yana karkashin kulawarsa kuma daga nan ne yake hana kauyukan sakat.

Yana daya daga cikin shugabannin ’yan bindigar da suka addabi Jihar Zamfara da sauran makwabtanta, a daidai lokacin da ta bayyana cewa mahukuntan jihar sun fi damuwa da siyasar zaben shekarar 2023.

Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshen Jihar Zamfara, Barista Bello Galadi, ya ce kauyuka da dama a jihar a yanzu ba sa karkashin kulawar gwamnati.

Dankarami da irin ta’addancinsa

Dankarami, wanda ake kira da Gwaska bai wuce shekara 30 da wani abu ba, amma yana jagorantar wani gungun ’yan bindigar da yawansu ba zai gaza 500 ba.

Ana kiran yaransa da ’Yan ShaBakwai, saboda yawancinsu matasa ne da suke da hannu a mafi yawan satar mutane da ta shanu a yankin da kuma kai farmaki kauyukan da suke yankin, kamar yadda wani wanda ya san Dankaramin ya shaida wa Aminiya.

Wani bidiyo da aka fitar a kafafen sada zumunta na zamani a kwanan nan ya nuna yadda Dankarami yake cin karensa ba babbaka.

A ciki dai an gano shi yana taro da shugabannin al’umma, cikinsu har da jami’an ’yan sanda, inda yake cika-baki a kan irin karfinsa, wanda ya hada da tarwatsa kauyuka da kuma kashe jami’an tsaro.

Majiyoyi masu tushe sun ce an haifi Dankarami ne wani kauye da ake kira da Lambar Gabas a Gundumar Rukudawa ta Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara, inda yanzu kuma ya mallaki wani katafaren gida mai daki 38 da masallaci da makarantar Islamiyya.

Gidan dai na da nisan kasa da kilomita biyu daga gabashin kauyen na Rukudawa, yankin da ya shahara wajen noma da kiwo a baya, amma yanzu matsalar tsaro ta kassara.

“Gidansa makare yake da ’yan bindiga dauke da miyagun makamai, kuma ya zama wata maboyar kowane irin bata-gari.

“A zahirin gaskiya ma, babu wanda zai yi kasadar zuwa wurin sai dai in daya daga cikinsu ne ko mai goyon bayansu,” inji majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda tsoron kai mata hari.

Rahotanni sun ce dan bindigar yana zaune ne tare da mahaifinsa wanda ake kira da Buda da kuma kakansa na wajen uwa wanda ake kira da Maiyara Dandela.

An kashe wani kawun Dankaramin da ake kira da Kundu a wata musayar wuta da aka yi a kwanakin baya.

“Ya addabi kowa a yankin da taimakon mahaifin nasa. Amma ba ya yarda su hadu da kakan nasa ido-da-ido saboda kokarin da yake yi na ganin ya shawo kansa ya -daina harkar ta’addnaci.

“Yana da yara a kusan dukkan dazukan kananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji a Jihar Zamfara da kuma Jibiya a Jihar Katsina, kuma su ne suka kai harin kauyen Dauran a Zurmi, inda aka yi awon gaba da shanu da raguna sama da 100,” inji majiyar.

Yayin da Dankarami da mahaifinsa suke zaune kusan koyaushe a gida, sauran danginsa kuwa, ciki har da mahaifiyarsa suna yawonsu yadda suke so, inda har mahaifiyar tasa rahotanni suka ce takan je cin kasuwa kusan duk ranar Lahadi a Zurmi.

Zaman lafiya ya gagara

Duk da yunkurin yin sulhun da gwamnatin Zamfara mai ci da wacce ta gabata da ’yan bindigar, Dankarami ba ya daga cikin wadanda suka taba halartar irin wannan tattaunawa. A wasu lokutan kuma yakan aike da wakilai.

A wani bidiyo da ya karade gari, an jiyo Dankarami yana ba da dalilian da ba ya son sulhu.

Ya ce, “Lokacin da muka dawo gida, sai na kira tsohon Sarkin da aka cire wanda yanzu haka yake Gusau cewa zan dawo in zauna lafiya da mutane.

“Zan zauna lafiya da iyayena, idan kuma wani abu ya sake faruwa a wani wurin, to babu hannuna a ciki. In kuma na saba alkawari to ya kira iyayen nawa ya sanar da su.

“Amma ya kekashe kasa ya ce ba zai zauna da dan bindiga ba. Tun lokacin na kashe wayata na kuma cire layin, ban sake amfani da ita ba. Da wayar yarana kawai nake amfani in zan yi kira,” inji shi.

Har yanzu dai mutane da dama na jin takaicin me ya sa hukuma ba za ta tunkare shi kai-tsaye ba.

Wani mazaunin Gusau, Mahe Abdulsalam ya ce, “Abin da ya fi ba kowa mamaki a bidiyon shi ne inda yake cewa ya kai wa sojoji hari, ya kashe su sannan ya kone motocinsu.

“A gaban ’yan sanda da jami’an gwamnati da ma wadansu masu rike da sarautun gargajiya ya fadi wannan. Abin takaici ne matuka. Ya zama kamar wani abin tsoro a idonsu,” inji Mahe.

Ko a kwanan nan, Aminiya ta gano cewa Dankarami ya yi fatali da yunkurin sulhu da malamin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya yi kokarin shiryawa.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa rashin imanin Dankarami ya karu ne tun lokacin da aka kashe kawunsa Kundu.

Kazalika, a baya yaransa sukan hau babura zuwa Zurmi, musamman a ranakun kasuwa, in ban da daga bisani da sojojin da aka girke a yankin suka fara fatattakar su duk lokacin da suka gan su.

Wadansu mazauna yankin sun bayyana mamakinsu a kan yadda aka gaza maganinsa, suna masu cewa tunda kasurgumin dan bindigar ba ya son duk wani yunkurin zaman lafiya, ba su ga dalilin da zai sa a kyale shi ya ci gaba da cin karensa babu babbaka ba.

“Abin takaici ne yadda hukumomi suka kyale shi yana yin abin da yake so a kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, duk da cewa an san maboyarsa,” inji wani mazaunin yankin.

“Me ya sa za a kyale shi ya ci gaba da yin abin da ya ga dama a kan mutane? Ya zama wajibi a yi wani abu a kan haka don magance matsalar nan,” inji shi.

Yadda Zamfara ta zama koma-baya

Jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohi mafiya koma-baya a bangaren ci gaba a Najeriya ta kusan kowace fuska, duk da tarin albarkatun kasa da Allah Ya albarkace ta da su da kuma kasar noma mai kyau.

A cewar alkaluman Hukumar Bunkasa Zuba Jari ta Kasa (NIPC), jihar tana da ma’adinin zinare da kusan kashi 30 cikin 100 na kasarta wacce za a iya nomawa da kuma wuraren yawon bude-ido.

Kazalika, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a rahotonta kan kudaden shiga na watanni shida na farko na 2020, jihar ce ta 20 a Najeriya inda take iya tara kudaden da ba su haura Naira biliyan bakwai ba.

NBS ta kuma ce ya zuwa watanni hudu na farkon bana, bashin da ake bin jihar ya kai kusan Naira biliyan 97, yayin da kason da ta karba daga asusun tarayya a 2020 ya kai Naira biliyan 41.

Kazalika, Kwamitin Shugaban Kasa da ke Duba Saukin Yin Kasuwanci na Kasa (PEBEC) a wani rahoton da ya fitar a kwanakin nan ya sanya jihar a matsayin ta 37 a jerin jihohin da suka fi saukin yin kasuwanci a Najeriya.

Abubuwan da kwamitin ya yi la’akari da su a rahoton sun hada da ababen more rayuwa da tsaro da samuwar bayanai da yanayin gudanarwa mai kyau da kuma wadatuwar ma’aikata.

A bangaren ilimi kuwa, Zamfara na cikin jerin jihohin da suka fi karancin daliban da suka samu sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da Ingilishi da Lissafi, yayin da kashi 11.95 cikin 100 ne kawai suka samu hakan a jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a shekarar 2018.

Daga Shehu Umar, Gusau da Sani Ibrahim Paki da Zahraddeen Yakubu, Kano da Taiwo Adeniyi, Abuja.