✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dani Alves ya cinye ayabar da aka jefe shi da ita

A karon farko a tarihin muzanta ’yan kwallo Dani Albes dan wasan baya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya sunkuya ya dauki…

A karon farko a tarihin muzanta ’yan kwallo Dani Albes dan wasan baya a kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya sunkuya ya dauki ayabar da wani mai goyo wa kulob din billareal baya ya jefe shi da ita kuma  ya cinyeta ba tare da nuna damuwa ba.
Al’amarin ya faru ne a karshen makon jiya a lokacin da kungiyoyin kwallon kafar biyu suka fafatawa a gasar rukunin La-Liga. na Sifen  A wasan, kulob din FC Barcelona ne ya samu nasara da ci 3-2.
Kafin lokacin, kulob din billareal ne yake kan gaba da ci 2-0 amma na FC Barcelona ya fanshe kuma ya zura kwallo ta uku ta wajen Lionel Messi.
Hakan ce ta harzuka wani mai goyon bayan kulob din billareal inda ya tattakura ya jefi Dani Albes da ayaba a matsayin zagi a daidai lokacin da yake kokarin bugun kusurwa (corner kick) amma dan kwallon ya sunkuya ya dauki ayabar  ya cinye ya cigaba da yin wasa ba tare da nuna wata damuwa ba.
Tuni hukumar shirya kwallo a Sifren FA ta zakulo mutumin da ya yi jifa da ayabar kuma ta hukunta shi.  An dakatar da shi daga shiga filin kwallo har  tsawon rayuwarsa don ya zam darasi ga masu niyyar aikata irin haka.