Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da kwamitin da ke aiki kan sayar da ɗanyen mai da man fetur a Naira.
Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun ne, ya jagoranci kwamitin zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
- Dalilin da ke haifar da jinkirin gyara wutar Arewa – TCN
- Ba za a caji ’yan Arewa kudin wuta ba —Minista
Cikin waɗanda suka halarta taron akwai Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mista Mele Kyari, Shugaban Hukumar Kula da Haraji (FIRS), Dakta Zacch Adedeji; da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Yemi Cardoso.
Sauran sun haɗa da Malam Farouk Ahmed daga Hukumar Kula da Man Fetur ta Ƙasa da ta Ƙasa (NMDPRA) da kuma Mista Gbenga Komolafe daga Hukumar Kula da Ma’adanan Mai na Ƙasa (NUPRC).
Bayan ganawar, ministan ya shaida wa manema labarai cewa sun tattauna kan shirin sayar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida a farashin Naira.
Ya bayyana cewa wannan shirin na shugaban ƙasa Tinubu ya samu ne sakamakon zuba jari mai yawa da Dangote ya yi a matatarsa.
Edun ya ƙara da cewa dukkanin masu ruwa da tsaki sun ɗauki alƙawarin ganin shirin ya samu nasara tare da magance duk wata matsala da ka iya tasowa.