✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista ta yi murabus kan ƙaryata mabarata

Ministar Kwadago da Jinkai ta kasar Cuba, Marta Feito Cabrera, ta sauka daga mukaminta bayan ta ce babu mabarata a kasar, sai dai masu karyar…

Ministar Kwadago da Jinkai ta kasar Cuba, Marta Feito Cabrera, ta sauka daga mukaminta bayan ta ce babu mabarata a kasar, sai dai masu karyar kasancewa mabarata.

Fadar Shugaban Kasar a ranar Laraba ta sanar da cewa Ministar ta amsa kuskurenta sannan ta mika takardar ajiye aiki kan abin da ta kira “nuna rashin rashin tausayi da rashin kwarewa a kan batun da yake da tasiri a siyasance a kasar.

Labarin dai na zuwa ne kwana daya bayan Ministar ta yi kalaman a gaban ’yan kwamitin majalisar kasar a kan talauci a kasar wacce tsibiri ce.

Marta dai ta ce, “Mun ga mutane, wadanda a Zahiri mabarata ne, amma idan ka kalli hannunsu, ka duba tufar da ke jikinsu, za ka ga sun yi bad-da-bami a matsayin mabarata, amma ba mabarata ba ne.

“A Cuba, babu mabarata,” in ji ta.

Ta kuma ce mutanen da ke wanke wa masu motoci gilashin motocinsu a kan titi suna rayuwa mai sauki, kuma sukan yi amfani da abin da suka samu wajen sayen barasa.

Nan take kalaman nata dai suka karade gari, musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika kiraye-kirayen ta ajiye mukaminta.

Kasar Cuba dai na cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki a ’yan shekarun nan.

Hatta Shugaban Kasar, Miguel Diaz-Canel sai da ya soki lamirinta.

Kasar dai ta shiga kangi ne tun bayan wani takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata a shekarar 1960, lokacin da Fidel Castro ya jagoranci juyin juya hali a kasar.