✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista

ukkanin ministocin ma'aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al'umma.

Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.

“Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba.

“Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi.

Kazalika ya soki shirin ‘yan siyasa na raba jari ga talakawa, yana mai cewa suna yi ne don boye gazawar gwamnati na samar da abubuwan more rayuwa da damarmaki ga al’ummarsu.