✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Dana ba ya cin abinci sai ayaba da ciyawa’

Ba ya cin abincin da aka dafa kuma gudun mutane yake yi.

Mahaifiyar Ellie ta ga ta kanta saboda yadda kullum take guje-guje dauke ta igiya tana bin shi a cikin daji, saboda yadda yake cin ciyawa yake kuma rayuwa kamar dabba.

Dattijuwar ta ce a kamo guda dan nata mai shekara 21 na yin yin gudun da ya haura kilimita 200.

A cewarta, ba ta da wani zabi face ta yi ta bin shi, saboda ba ya maganaga kuma ba ya cin abincin da take girkawa, maimakon haka, ayaba da ’ya’yan itatuwa da kuma ciyayi kawai yake ci kauyen nasu da ke kasar Rwanda.

Mahaifiyar Ellie wadda take cikin tsananin damuwa ta ce haka dan nata ya shiga ranta sosai kuma tana ganin shi a matsayin wata baiwa daga Allah, saboda ’ya’ya biyar da haifa kafin shi duk sun rasu ne suna  ne kanan.

Sai dai ta ce tunda ta haife babu abin da yake iya koyo, saboda haka ko makaranta ba ya zuwa, hasali ma tsoron mutane yake yi. Dabi’un Ellie da suka saba wa na dan Adam ya sa wasu ke kiran shi ‘biri’ ko ‘mutumin daji’.

Mahaifiyarsa ta ce: “Ba ya son abinci, ya fi son ayaba, babu abin da ya iya in banda gudu; Da ya ga mutane sai ya fara gudun su.

“Idan ya fara wannan gudun kuma dole sai ni ma na bi shi. A mako muna iya shafe kusan kilomita 230 da shi. Ina tsoron idan ban bi shi ba wata rana ba zai dawo gida ba.”

A bidiyonsa da gidan talabijin na Afrimax TV ya nuna, an ga yadda mutane ke ta fadi-tashin ganin ya bar shiga daji kuma ya kasance cikin aminci.

Makwabtansu a kauyen ma suna taimakawa wajen lura da Ellie da kuma lura da idan ya shiga idan ya fara guje-gujen, domin tabbatar da bai fada cikin wani hadari ba.

A bidiyion mahaifiyarsa ta ce: “Yana kiwo ne kamar dabba, yana kuma tserewa.”

Saboda tsananin gudun Ellie a cikin daji, ana kwatanta shi da fitaccen dan tseren duniya, Usain Bolt, sai dai shi bai iya managa ba sai dai kurmanci.

Saboda haka ne mahaifiyarsa ta take yawo da igiya domin kamo shi — a duk lokacin da ya nemi ya yi kokarin guje-gujen, sai ta bi shi ta zargo shi da igiya.

A lokacin da aka haifi Elli, kansa bai wuci girman kwallon tenis ba, kamar yadda bidiyion bincike na ‘Born Different’ ya nuna.

Mahaifiyarsa ta shaida wa masu binciken cewa: “Bayan mutuwar ’ya’ya biyar da muka haifa sai muka roki Allah Ya kara ba mu da ko da nakasasshe ne, matukar dan ba zai rasu da wuri ba kamar sauran. Da Allah Ya ba mu shi kuma na san wani sako ne daga Ubangiji.”

Ta ce makwabta ba sa daukar sa a matsayin da, kallon shi suke yi a matsayin biri kuma suna yawan cin zalin shi.

Amma “Ina jin takaici a duk lokacin da ya fita ya dawo an dake shi. Suna masa tsawa suna kiran shi biri. Ina bakin cikin jin ana zaluntar shi,” inji mahaifiyar Ellie.

%d bloggers like this: