A makon jiya ne dan tseren babur, dan kasar Japan mai suna Matsushita Yoshinari ya mutu a lokacin da gasar tseren babur ke gudana a kasar Ireland ta Arewa (Northern Ireland).
Shahararren dan tseren ya gamu da ajalinsa ne bayan sun yi zubar gade da daya daga cikin wadanda suke fafatawa.
Marigayi Matsushita, mai kimanin shekara 43 ya rasu ne jim kadan bayan an garzaya da shi asibiti.
Kafar sadarwar mailonline.com ta kalato mahukunta da suka shirya gasar sun dakatar da ita saboda abin da ya faru kuma tuni suka aika da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.
Marigayi Yoshinari da ya fito daga yankin Saitama na kasar Japan ya fafata a gasar tseren babur ta shekarar 2009 inda ya zo na biyar. Sannan shi ya lashe gasar da ta gudana a shekarar 2008 da ta gudana a yankin Motegi a Japan.
Wata sanarwa da mahukuntan da ke shirya gasar suka aika ta yanar gizonsu tana dauke ne da sakon ta’aziyyar kamar haka: “Muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamaci Yoshi da kuma abokansa, muna fata za su yi hakurin jure wannan gagarumin rashi da muka yi”.
Shi kuma daya daga cikin masu kula da yadda gasar ke gudana mai suna Gary Thompson ya bayyana Yoshi a matsayin babban rashi ga daukacin masu gudanar da gasar tseren babur musamman masoyansa da abokan hamayyarsa. “Mutum ne da ke haba-haba da kowa, hasalima za a dade ba a manta da shi ba”.
Tuni hukumar gudanar da gasar ta fara gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar hadarin.
Dan tseren babur Matsushika ya mutu a hadari a lokacin da ake gasar tsere
A makon jiya ne dan tseren babur, dan kasar Japan mai suna Matsushita Yoshinari ya mutu a lokacin da gasar tseren babur ke gudana a…