✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar Gwamnan PDP ya tsallake rijiya da baya a Zamfara

Dan takarar ya ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a tawagar matarsa.

Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara a Jam’iyyar PDP, Dauda Lawal Dare, ya tsallake rijiya da baya bayan gungun wasu ’yan daba suka yi yunkurin kashe shi da matarsa.

Ya shaida wa manema labarai cewa an kashe ’yan sanda biyu, wasu kuma sun samu munan raunuka a tawagar matarsa a daren ranar Alhamis.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare a lokacin da matarsa ​​da tawagarta ke dawowa daga unguwar Tudun wada da ke cikin birnin Gusau.

“Ina kira a gare ku da akai rahoton harin da ya faru jiya da misalin karfe 11:30 na dare inda wasu suka kai wa tawagar matata hari, sun kashe jami’an tsaro guda biyu da ke tare da ayarin, sun kuma jikkata wasu a daidai gidan man AA Rano da ke Tudun Wada.”

Ya cewa hare-haren da ake kai wa ’ya’yan jam’iyyar na daga masa hankali don haka ya yi kira ga Shuganan ’Yan Sanda da jami’an Sibil Difens da sauran hukumomin tsaro da su yi cikakken bincike tare da tabbatar da an yi adalci.

Ya kuma roki magoya bayan jam’iyyar a jihar da su kwantar da hankalinsu sannan su daura damarar kada kuri’a a zaben ranar Asabar.

Da yake mayar da martani kan zargin kai harin, Kwamandan yaki da ’yan daba na Jihar Zamfara, Bello Bakyasuwa, ya bayyana zargin a matsayin maras tushe.