Dan takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PRP a zaɓen da ya gabata, Salihu Tanko Yakasai, ya sake komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Ya sanar da hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Kafin ficewarsa daga APC a 2022, Salihu dai ya rike muƙamin Hadimin tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma shugaban APC na ƙasa mai ci, Abdullahi Umar Ganduje.
A cikin sakon, Salihu ya ce, “Mai Girma Shugaban Jam’iyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci da mu dawo Jam’iyar APC domin ba da gudunmawa wajen inganta ta, da ciyar da ita gaba, kuma tuni muka amsa wannan kira nasa.
“Saboda haka nake sanar da ficewa ta daga Jam’iyar PRP mai alamar dan mabudi, da kuma komawa ta jam’iyar APC.
“Na bada wannan a rubuce zuwa ga Jam’iyar PRP a matakin mazaba ta da kuma jiha, sannan zan kuma sake yankar katin APC da yardar Allah,” in ji shi.
Ganduje dai ya cire Salihu daga mukaminsa ne a wancan lokacin saboda sukar salon mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Bayan cire shi ne kuma daga bisani ya sanar da ficewa daga APC zuwa PRO, daga baya kuma yi mata takarar Gwamnan Kano, amma bai yi nasara ba.