✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AU ta kira taron gaggawa kan juyin mulkin Gabon

A karon farko an Mista Bongo, wanda sojojin da suka yi wa juyin mulki ke tsare da shi da iyalansa

Sojojin Gabon sun sanar cewa a ranar Laraba za su sanar da wanda zai jagoranci kasar, a yayin da kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta kira taron gaggawa kan juyin mulkin kasar.

Kwamandan rudunar tsaron shugaban kasar, Brice Oligui Nguema, ya sanar cewa Janar-janar din sojin kasar za su yi zama a ranar inda za su ayyana wanda zai jagoranci gwamnatin sojin.

Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kwamitin zaman lafiya na kungiyar AU Willy Nyamitwe ya sanar a ranar cewa za su yi taron gaggawa a da kasashen Burundi, Senegal da Kamaru kan lamarin kasar Gabon.

Ya yi jawabin ne bayan hamɓararren Shugaban Gabon, Ali Bongo ya roƙi ƙasashen duniya su kawo ɗauki bayan sojojin ƙasar sun yi masa juyin mulki.

Sai dai wasu jama’ar kasar na ta murna inda suka fito kan titunan birnin Brazeville tare da sojojin suna rera taken kasar da kuma yaba wa sojojin bisa juyin mulkin.

Wani bidiyo ya nuna daruruwan sojoji cikin murna sun daga kwamandan rundunar tsaron fadar shugaban kasar a kafadunsu, suna masa kirarin ‘Shugaban Kasa’ jim kadan bayan kifar da gwamnati da kuma tsare Mista Bongo.

Sojojin sun tsare Ali Bongo a Fadar Shugaban Kasa, inda daga nan ake kyautata zaton ya fitar da saƙon bidiyon da yake neman ɗaukin.

“Ina kira ga duk abokan ƙasarmu a faɗin da cewa su yi magana a kan abin da ke faruwa (…) kan waɗannam mutane da suka tsare Ni tare da iyalaina.” in ji shi a cikin bidiyon da aka gan shi cikin tsananin damwua.

Ya bayyana cewa ana tsare da shi ne a cikin gidansa, amma matarsa da ɗansa kuma suna tsare a wani waje daban.

Karon farko ke nan da aka ji ɗuriyar Bongo wanda sojoji suka hamɓarar ’yan sa’o’i bayan ya lashe zaɓen da zai fara wa’adin mulkinsa na uku, bayan ya gaji mahaifinsa a 2009.

Jama’ar Gabon na murna da Juyin mulki

A sassan ƙasar dai jama’a na ta bukukuwa domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin.

Hasali ma, rundunar tsaron ƙasar ta sanar da goyon bayanta ga shugaban rundunar tsaron fadar gwamnati kan juyin mulkin.

Sojojin dai sun soke zaɓen da Bongo ya lashe, tare da rushe masu riƙe da muƙaman siyasa kuma sun rufe iyakokin ƙasar, bayan juyin mulkin na ranar Laraba.

Idan juyin mulkin Gabon ya tabbata, zai zama na takwas da sojoji suka yi cikin shekara uku a nahiyar Afirka, kuma duk ƙasashen da Faransa ta raina a baya.