✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rusau: Wike ya markaɗe Kasuwar Dare a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya rushe Kasuwar Dare da ke yankin Sabuwar Asokoro a Abuja.

Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya rushe Kasuwar Dare da ke yankin Sabuwar Asokoro a Abuja.

Ministan yaba da umarnin rushe Kasuwar ne bisa zargin ta da zama matattarar dillalan miyagun ƙwayoyi da ’yan dana da sauran masu aikata laifuka.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito  Darakta Kula da Gine-ginen a Birnin Tarayya, Mr Mukhtar Galadima, na cewa kasuwar ta fara zama barazana ga mazauna yankin da ma masu wucewa.

Mukhtar Galadima ya ce duk da ƙoƙarin da Hukumar Kula da Birnin Tarayya take yi na samar da aminci a birnin, Kasuwar Dare ta zama sansanin masu aikata laifi.

Kasuwar dai tana kan titin Hassan Musa Katsina, kusa da Kpaduma II a Sabon Asokoro.