✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar APGA ya lashe zaben cike gurbi a Jihar Neja

(INEC) ta ayyana dan takarar jam'iyyar APGA, Shehu Sale a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi a mazabar dan Majalisar Tarayya ta Magama/Rijau

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APGA, Shehu Sale a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi a mazabar dan Majalisar Tarayya ta Magama/Rijau a jihar Neja.

Hukumar ta ce dan takarar ya lashe zaben ne na ranar Asabar bayan ya sami kuri’u 22,965 inda ya doke abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Alamu Emmanuel wanda ya sami kuri’u 22,505.

Baturen zaben, Farfesa Tanko Baba na Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato wanda ya bayyana sakamakon ya kuma ce dan takarar jam’iyyar ADC, Yusuf Nasir ya zo na uku bayan ya sami kuri’u 336.

Ya kara da cewa adadin yawan masu rijista a zaben sun kai 159,347, wadanda aka tantance 46,734, kuri’un da aka kada 46,499 sai kuma wadanda suka lalace  guda 691.

A wani labarin kuma, Kwamishinan Zabe na Jihar Neja, Farfesa Samuel Egwu ya yabawa masu zabe a mazabar kan yadda zaben ya gudana lami lafiya.

Ya kuma jinjinawa rawar da jami’an ‘yan sanda suka taka wajen samar da tsaro yayin zaben.