Mai neman Jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, Adamu Garba, ya bayyana kaduwarsa da jin farashin fom din takararar da jam’iyyar ta saka na Naira miliyan 100.
Adamu Garba ya bayyana kaduwar tasa ce a shafinsa na Twitter bayan sanarwar farashin kudin fom din takarar da jam’iyyar ta fitar.
- Hatsarin jirgin sama 11 da suka kashe hafsoshin sojin Najeriya
- Yadda Benzema yake kwatar Real Madrid a bana
“Miliyan 100 kuɗin fom. Lallai!,” kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na Twitter.
Sai dai matashin dan siyasar ya yi gugar zana sannan ya ja hankalin matasa da su fito a goga da su a harkar siyasa.
“Ba zai yiwu mu ci gaba da sayen ofisoshin gwamnati a Najeriya ba, muna bukatar shugabanni na kwarai a 2023,” a cewarsa.
Sanararwar kudin sayen fom din takarar neman kujeru daban-daban da jam’iyyar APC ta fitar ya bar baya kura.
Mutane da dama na ganin cewar jam’iyyar ba ta shirya tafiya da matasa ba, ganin makudan kudaden da ta sanya wa fom din takara.
Tuni mutane a kafafen sada zumunta da na watsa labarai suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan sanarwar kudin fom din takarar kujerar shugabanci na jam’iyyar APC.
Amma APC ta yi rangwame ga mata da nakasassu da ke burin tsayawa takara, inda ta ba su damar samun fom din takara kyauta.
Duk da haka za su sayi fom din bayyana aniyarsu ta fitowa takara.