Wani mutum mai shekara 52 a duniya, ya shiga hannun rundunar ’yan sanda a Jihar Ondo kan zarginsa da laifin kwanciya da ’yarsa mai shekara 19.
’Yar mutumin ta yi ikirarin cewa mahaifin nata ya saba lalata da ita idan dare ya raba tun ba ta wuce shekaru 13 a duniya ba.
- Rikicin aure ne matsalar da aka fi kawo wa Hisbah a Kano
- Za a rufe kasuwar Wuse da ke Abuja saboda karya dokar COVID-19
- Ina da shakku a kan ingancin rigakafin cutar Coronavirus — Sheikh Jingir
A cewarta, mahaifinta ya rika tashinta cikin duhun dare sannan ya kaita dakin dahuwar abinci na gidansu inda yake keta mata haddi.
Ta ce, “mahaifina ya rika nema na lokaci zuwa lokaci inda a wani sa’ilin idan naki amincewa da bukatarsa sai dai na kwana a waje.”
Dubun wanda ake zargi ta cika a ranar 24 ga watan Dasumba yayin da ya kai ’yar tasa Otel din Hayyana da ke yankin Owo na Jihar domin aikata fasadi na biyan bukatarsa da ita kamar yadda ya saba.
Mutumin ya amsa laifinsa bayan shigarsa hannu, sai dai ya ce sau daya ya taba kwanciya da ita kuma ya alakanta lamarin da sharrin Shaidan.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, Mista Tee Leo Ikoro ya inganta rahoton wanda a cewarsa suna ci gaba da gudanar da bincike domin kuwa wannan ba lamari ne da za a yi sanyin jiki a kansa ba.
Ya ce, “za mu yi iyaka bakin kokarinmu wajen ganin hukunci na shari’a ya tabbata a kan wanda ake zargi saboda wannan mummunar aika-aika.”