Tsautsayi da ba ya wuce ranarsa inji Hausawa ya sa wani yaro dan shekara biyar ya rasa ransa a cikin wata motar dakon daliban makaranta a yankin Qatif na Kasar Saudiyya.
Wannan abun bakin ciki dai ya faru ne bayan rafkanuwa ta kama direban motar wanda ya manta bai tabbatar da duk daliban da ya dauka sun sauka ba.
- Akwai kamanceceniya tsakanin Masarautar Kano da ta Ingila —Nasir Khalil
- Buhari zai karrama Dakta Bashir Umar da lambar OON
Bayanai sun ce, direban bai lura cewa dalibin wanda bai dade da fara makaranta ba yana ta sharar barci a cikin motar har aka rufe shi a ciki ba tare da an ankara ba.
Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, wannan lamari ne ya yi ajalin yaron saboda rashin samun iskar da zai shaka la’akari da cewa ko’ina rufe yake a motar kuma ana kwala rana.
Rahotanni sun ce tsananin zafi da aka fuskanta a yankin Qatif ya kai kusan digiri 40 a ma’aunin Celsius a ranar Lahadi.
Tuni dai bincike ya kankama a kan lamarin, inda mahukunta ke fadi-tashin kai wa da komo wa tsakanin makarantar da abin ya faru da sauran wuraren da abin ya shafa.
Kafar watsa labarai ta Al Arabiya ta ruwaito cewa, ana ci gaba da aike wa iyayen yaron sakonnin ta’aziya hadi da bayyana alhini dangane da rashin da suka yi.