Wani saurayi dan kimanin shekara 16 mai suna Eammanuel Obuh ya zama zakara a gasar tsere ta ’yan sakandare da Gwamnatin Jihar Legas ta shirya wa daukacin makarantun sakandare da ke fadin jihar da aka yi wa lawabi da “Ibile Games”. Yanzu matashin ne ya kafa sabon tarihi a gasar tseren makarantun sakandaren da ke daukacin fadin kasar nan.
A gasar, Emmanuel Obu ne ya zama zakara a tseren mita 800 da kuma a gudun fanfalakin mita 1,500.
An gudanar da gasar a ranar Alhamis din makon jiya a harbar Jami’ar Legas kuma ta samu halartar daukacin makarantun sakandare daban-daban da ke fadin jihar.
Emmanuel da ke ajin karatu na SS2 a makarantar sakandare ta ISL, ya samu nasarar lashe gasar tsreren mita 800 ne a tsawon minti biyu da dakika 9 yayin da ya lashe ta mita 1,500 a tsakanin minti 4 da dakika 39 al’amarin da ya sa ya kafa sabon tarihi a gasar tseren makarantun sakandare a fadin kasar nan.
Matashin ya ce yanzu burinsa shi ne ya wakilci Najeriya a gasar Olamfik kuma yana hankoron ya lashe zinare a gasar.
Ya ce bai taba tunanin zai zama zakara a gasar tseren makarantun sakandare da ke Legas ba, amma dai ya ya yi amanna cewa yadda ya rika bayar da himma wajen nuna kwazo a atisaye kafin gasar ya taimaka masa wajen samun nasara.
Ya yi fatan ya cigaba da nuna kwazo don ganin ya yi fice a gasar tsere a ciki da wajen Najeriya.