✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dan gidan Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya rasu

Abdulmakilin dan gidan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya rasu

Allah Ya yi wa Abdulmalik dan gidan marigayi Shekh Ja’afar Mahmuud Adam rasuwa a ranar Asabar 10 ga Oktoba, 2020.

Da yake tabbatar da rasuwar, Sheikh Gadon Kaya ya ce Abdulmaki ya rasu ne a hatsarin mota kuma za a yi masa jana’iza a masallacin Usman bn Affan da ke Kofar Gadon Kaya, daya daga cikin majalisan karatun Sheikh Ja’afar a lokacin rayuwarsa.

Ministan Fasahar Tattalin Arziki na Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami na daga cikin wadadan suka sanar da rasuwar dan gidan shehin malamin a sakon ta’aziyar da ya wallafa ta shafinsa na Facebook.

“Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH).

“Ina mika ta’aziyya zuwa ga ’yan uwansa da iyayensa kan Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran ’yan uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan na su.

“Wanda ya mutu, bai yi sauri ba. Mu da muke nan ba mu dade ba, sai mun zo in sha Allah”.

“Za’aji lokacin jana’iza insha Allah; Muna kara addu’a Allah Ya gafarta masa Ya ba shi Firdausil A’alah”, inji a wani sako da ke tabbatar da rasuwa Abdulmalik Ja’afar daga majalisin Sheikh Bashir Aliyu Umar na karatun littafi Sahihul Bukhari.

Malamai sun alhijin rasuwa AbdulMalik Ja’afar

Farfesan Sheikh Mansoor Ibrahim Sokoto ya ce, “Yanzu muke samun labarin mun rasa danmu AbdulMalik Jafar Mahmud Adam a cikin wani hatsarin mota.

“Ya Allah Ka yi masa gafara. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.

Sheikh Gadon Kaya a nasa shafin na Facebook ya wallafa cewa; “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un.

“Abdulmalik Ja’afar Mahmud Adam ya rasu yanzu”.