Masu Keke-NAPEP sun tare babbar hanyar Nnamdi Azikiwe da ke Kaduna na tsawon sa’o’i bayan wani dan sanda ya bude wa fasinjojin wani Keke-NAPEP wuta.
Lamarin da ya faru a safiyar Laraban ya janyo zanga-zanga inda ’yan Keke NAPAEP suka rufe babban titin wanda ya tilasta wa sauran masu ababen hawa canza hanya, kafin daga bisani aka sake bude hanyar.
- Dalibai fiye da 400 da suka karanci likitanci a ƙetare sun faɗi jarrabawar samun lasisi
- HOTUNA: Zanga-zanga ta barke a Kano kan soke nasarar Abba Gida-Gida
Shaidu sun bayyana cewa ’yan sandan sun biyo Dan Keke NAPEP din ne daga Unguwar Mu’azu har yankin Anguwar Nasarawa da nufin kama shi.
Amma da ya ki tsayawa sai daya daga cikin ’yan sandan ya bude wuta har ya raunata mutum biyu da ke cikin keken, namiji da wata mace.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya shaidawa Aminiya cewa dan sandan da yi harbin tuni an kama shi.
Ya kuma bayyana cewa wayanda suka samu rauni an kai su asibiti domin duba lafiyarsu, har an sallami macen daga asibitin bayan an duba ta.
A ranar Larabar ce aka samu irin wannan zanga-zanga a Kano, bayan wani dan sanda ya bude wa wasu mutum biyu wuta ya kashe daya daga cikinsu a unguwar Kurna Asabe.
Dan sandan ya bude wuta ne a lokacin da suka je kwantar da rikicin ’yan daba unguwar.
Shaidu sun ce dan sandan ya ya yi harbi ne bayan kurar ta lafa, har bata-garin sun bar wurin.
Amma kuma wanda dan sandan ya kashe, kowa ya san shi mutumin kirki ne, ba shi da wata alaƙa da bata-garin, wanda hakan ya harzuka mutane suka yi zanga-zanga suka tare hanyar zuwa Katsina na tsawon lokaci.
Kwamishinan ’yan sandan Kano, Hussaini Muhammad Gumel ya ce dan sandan ya yi har bin ne ba tare da izini ba, don haka an cafke shi.
Bisa alama dai jami’in ya rasa kakinsa.